| Hausa
AFIRKA
4 MINTI KARATU
Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan'adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.
Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu
Attajirin ya ce ya so yin wannan ziyara tun da jimawa amma yawan tafiye-tafiyensa suka sa sai yanzu ya zo. / Others

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan'adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.

Dangote ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Jihar Kano, a ranar Juma’a, inda ya ce ya yi amanna talaka na cikin ƙunci kan halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

Attajirin ya ce ya so yin wannan ziyara tun da jimawa amma yawan tafiye-tafiyensa suka sa sai yanzu ya zo.

Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano don inganta kiwon lafiya da ilimi da karfafa wa masu karamin karfi da ke gwagwarmayar rayuwa, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan ganawar ta ce.

“Da farko dai mun zo nan ne don mu taya ku murnar nasarar da kuka samu a Kotun Ƙoli, ina so in tabbatar muku da goyon bayanmu a tsawon mulkinku, watakila ba shekara hudu kawai ba har amma shekaru takwas.

Dangote wanda ya ce Kano gida ne a wajensa, duk da cewa mai gabatarwa a wajen taron ya bayyana shi a matsayin baƙar fatan da ya fi kuɗi a duniya, ya ce “Ni naku ne don haka koyaushe za ku iya kira na don hadin kai kan yadda za mu ciyar da Kano gaba.”

"Kuma a ci gaba da gaske muna bukatar ganin yadda za mu bunkasa fannonin kiwon lafiya da ilimi da ƙarfafa wa gwamnati, da ta yadda za mu taimaka wa gwamnati domin gwamnati ba za ta iya yin komai ita kadai ba".

Dangote ya ci gaba da shaida wa Gwamna Abba cewa "Akwai haƙƙin mutane a kanku kuma a yanzu jama'a na cikin matsi. Don haka a yanzu ku ne za ku zama majinginar mutane mu kuma za mu taya ku ji da su.

“Don haka ku tabbata cewa za mu ba ku goyon baya kuma za mu goyi bayan gwamnatinku, kuma muna so mu gaya muku cewa za mu ci gaba da yi muku addu’ar samun nasara domin nasararku tamu ce.

Bayanin Abba K Yusuf

A nasa bangaren, Gwamna Yusuf Yusuf ya nemi goyon bayan attajirin kan kafa cibiyar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfado da masana’antun da suka lalace da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Hakazalika, Gwamnan ya shaida wa Dangote Kano cewa yana matukar bukatar a kafa asibitin masu cutar sikila a jihar domin samar da magunguna kyauta ga marasa lafiya.

Baya ga haka, sanarwar ta ce Abba Gida-Gida ya roƙi hamshaƙin ɗan kasuwan cewa "ka daure ka kammala manyan ayyukan da gidauniyarka ta Dangote ta ƙaddamar wadanda suka hada da sashen gaggawa da dakin tiyata da sashen mata masu juna biyu da na yara duk a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhamnad."

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaban riƙon jihar Kudu maso yammacin Somaliya zai hau kan mulki bayan ajiye aikin shugaba