| Hausa
AFIRKA
4 MINTI KARATU
Gwamnatin Jihar Kano ‘ba za ta yi katsalandan a shari’ar da ake yi wa Murja Kunya ba’
Gwamnati tana sane da cewa batun na doka ne da yake cikin tsarin shari'a kuma ba za ta taɓa yin katsalandan ta kowace hanya don yin tasiri wajen samar da adalci ba.
Gwamnatin Jihar Kano ‘ba za ta yi katsalandan a shari’ar da ake yi wa Murja Kunya ba’
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba za ta yi katsalandan a cikin shari’ar da ake yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan Mruja Kunya ba. Hoto: Abba K Yusuf Facebook / Others
19 Fabrairu 2024

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce ba za ta yi katsalandan a cikin shari’ar da ake yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan Mruja Kunya ba.

“Sai dai an shaida wa gwamnati cewa an sake samun wani sabon zargin da ake yi mata wanda ya sa jami’an tsaro suka fitar da ita daga gidan gyaran halin domin bincike” a cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun Kwamishina Watsa Labarai, Baba Halilu Dantiye a ranar Litinin.

Ta kuma ce har yanzu shari'arta ba ta mutu ba, kuma za ta ci gaba har zuwa matakin ƙarshe da kotu za ta yanke hukunci,

Gwamnatin ta ce ta fitar da sanarwar ce saboda “An jawo hankalin gwamnatin Jihar Kano kan wani zargi mara tushe da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta kan cewa da hannunta a sakin Murja Ibrahim Kunya da aka yi daga gidan yari, wacce take fuskantar shari’a a kan watsa bidiyon da suka take wasu dokokin jihar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “waɗannan zarge-zarge kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, wani hasashe ne marar tushe na wasu ɓata-gari da suke so su baƙanta gwamnati da Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf a idon al’umma.

A makon da ya gabata ne Hukumar Hisbah a Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya inda har ta gurfanar da ita a gaban kotu bisa wasu zarge-zarge da suka haɗa da yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.

Kotun ta tura ta gidan gyaran hali da niyyar zuwa ranar da za a koma sauraron shari’ar, amma daga baya hukumar gidan yarin ta sake ta bayan da ta ce ta samu takardar daga kotu.

Gwamnatin jihar ta ce tana sane da tanadin da kundin tsarin mulkin kasar ya yi na raba madafun iko da ma’auni tsakanin bangaren shari’a da na majalisa da na zartarwa a matsayin bangarori uku na gwamnati, kuma ba za ta taɓa yin wani abu da zai kawo cikas ga wannan tsari ba.

Gwamnati tana sane da cewa batun na doka ne da yake cikin tsarin shari'a kuma ba za ta taɓa yin katsalandan ta kowace hanya don yin tasiri wajen samar da adalci ba.

Sanarwar gwamnatin ta kuma tunatar da al’umma cewa abin da ta sani a kan batun shi ne cewa an gurfanar da Murja Kunya a gaban wata Kotun Shari’a da ke Kwana Hudu a karamar hukumar Nassarawa bisa zargin ta da yada wasu munanan bidiyoyi a dandalin sada zumunta, inda kotu ta bayar da umarnin hakan tare ta a gidan gyaran hali kafin a ci gaba da sauraron shari’ar a ranar Talata, 20 ga Fabrairun 2024 bayan ta saurari bukatar neman belinta.

A ƙarshe gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi mata, tana cewa ba wani abu ba ne illa ƙoƙarin ɓata mata suna tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar tanadin kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaban riƙon jihar Kudu maso yammacin Somaliya zai hau kan mulki bayan ajiye aikin shugaba
Sudan ta nemi 'yan ƙasar da suka yi ƙaura zuwa ƙasashen waje saboda yaƙi su koma gida