| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo ta nada tsohon dan bindiga Ministan Tsaro
Wannan yunkuri ya zo ne bayan da kasar ta sha fama da rikice-rikicen ‘yan bindiga, sannan kuma take fuskantar zabuka da za a yi a Disamba, inda Shugaba Tshisekedi zai nemi karin wa’adin mulki.
Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo ta nada tsohon dan bindiga Ministan Tsaro
Kotun ICC ta taba yanke wa Jean-Pierre Bembe hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 / Photo: AFP / AFP
24 Maris 2023

Shugaban kasar Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, Felix Tshisekedi ya nada tsohon shugaban kungiyar ‘yan bindiga, Jean-Pierre Bemba a matsayin Ministan Tsaro, biyo bayan wata kwaskwarima da ya yi wa gwamnatinsa.

Wannan ya zo ne yayin da rikice-rikicen ‘yan bindiga ke addabar yankin gabashin kasar.

Kotun kasa da kasa ta ICC ta taba yanke wa Jean-Pierre Bembe, wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasa tsakanin 2003 zuwa 2006, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10.

Amma a shekarar 2018, kotun ta yi watsi da wancan hukuncin. Jean-Pierre Bemba zai maye gurbin ministan tsaro na yanzu, wato Gilbert Kabanda.

Haka nan, an nada tsohon shugaban ma’aikatar fadar Shugaba Tshisekedi, wato Vital Kamerhe a matsayin Ministan Tattalin Arziki.

An taba hukunta shi da laifin almubazzaranci inda aka yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan kaso. Amma daga baya kotu ta wanke shi, sannan ya samu ‘yanci a shekara daya bayan haka.

Mutanen biyu da aka yi wa sabon nadin, ba sa cikin jam’iyyar Shugaba Tshisekedi, mai suna Union of Democracy and Social Progress (UDSP).

Wannan mataki ya zo ne a yayin da kasar ke shirye-shiryen zaben da za a yi a watan Disamba na wannan shekarar, a inda ake kyautata zaton shugaban zai samu sabon wa’adi.

Lokacin sanar da nadin a gidan tabaijin na kasar ranar Alhamis, mai magana da yawun shugaba Tshisekedi ya ce, kwaskwarimar da aka yi wa gwamnatin tana da “alfanu matuka” ga kasar, musamman idan an duba “kwarewar” sabbin ministocin.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Nijar ta ƙaddamar da sabon katin ɗan ƙasa na zamani mai tambarin AES
Laifi mafi muni: AU ta nemi MƊD ta ɗauki mataki kan biyan diyyar cinikin bayi bayan MƊD ta tabbatar
Ghana ta sake yin bita kan tsarin yaƙi da ta’addanci sakamakon barazanar masu tsattsauran ra’ayi
Rasha ta yi iƙirarin cewa 'yan kwangilar sojin Faransa na da yawa a Afirka
Hukumomi a Nijar sun kama wani mutum a Zinder bisa zargin yawan kai wa 'mata' hari a kan babur
Me ya sa diyyar cinikin bayi da mulkin mallaka suka zama masu muhimmanci ga Afirka a 2026
Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutane tara, wasu da dama sun ɓata a gaɓar tekun Djibouti
MDD ta ayyana cinikin bayi a Afirka a matsayin ‘laifi mafi muni ga ɗan'adam'
Shugaban Ghana ya faɗa a New York cewa Amurka tana goge tarihin baƙar-fata
Iskar kasar Chadi ce mafi muni da rashin inganci a Afirka a 2025 - Rahoto
Ranar Tarin Fuka ta Duniya: Yadda injinan GeneXpert suke sauya yaƙi da cutar TB a Togo da Congo
Ghana ta buƙaci taimakon MDD don warware batun cinikin bayi saboda ƙarfafa ƙoƙarin neman biyan diyya
Makomarmu ba ta sayarwa ba ce: Abin da ya sa dole matasan Afirka su nemi ba’asin haraji da cin bashi
Me ya sa yawancin tutocin kasashen Afirka suke da kamanceceniyar kaloli?
Aƙalla mutum 81 sun mutu cikin makonni sakamakon ambaliyar ruwa a Kenya
An kashe mutum 64, cikinsu har da ƙananan yara 13, a harin asibitin Sudan — WHO
Eid al-Fitr: Hotunan yadda aka yi bikin ƙaramar Sallah a ƙasashen Afirka
Nijeriya ta zama ta huɗu yayin da Sahel ke kan gaba a yawan kashe-kashe na ta'addanci —Rahoto
Yadda duniya ta rungumi shan gahawa kuma manoma a Afirka suke samun alheri
An kawar da mazan jiyan Kamaru yayin da majalisar dokokin ta zaɓi sabbin shugabanni