| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kotu ta daure sojan Amurka na bogi a Kaduna
Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfara.
Kotu ta daure sojan Amurka na bogi a Kaduna
Alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar da matashin ya yi amfani da ita wurin yaudara. / Hoto:Reuters / Others

Hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Kasa, EFCC, ta ce kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu kan samun shi da laifin yi wa rundunar sojin Amurka sojan-gona.

Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ne ya yanke masa hukunci bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa guda daya da ake zarginsa da aikatawa.

Bayan yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu, Mai Shari’a Khobo ya ba shi zabin biyan tarar naira 150,000.

Sannan alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar Kassah wato Samusng Galaxy A02 wadda ya yi amfani da ita domin aikata laifin.

Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfara.

Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’a.

Zamba cikin aminci da yaudara na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta EFCC ke yaki da su a Nijeriya.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta EFCC ta kama wani matashi wanda ake zargi da yi wa matar Sarkin Bichi zamba cikin aminci ta naira miliyan 20.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru
Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara