| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Nakiya ta kashe sojoji bakwai a Jamhuriyar Nijar
Harin ya auku ne ranar Lahadi a garin Tillaberi, inda motar soji ta taka nakiyar da aka binne a hanya.
Nakiya ta kashe sojoji bakwai a Jamhuriyar Nijar
Sojin Nijar suna fuskantar karin hare-hare a baya-bayan nan / Hoto: Getty Images / Getty Images

Hukumar Tsaron Kasa ta Jamhuriyar Nijar ta ce sojojin kasar bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon taka nakiyar da aka binne a hanya ranar Lahadi, a yankin Tillaberi.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce lamarin ya rutsa da motar soji mai safarar kaya mako-mako a yankin da ke da nisan kilomita shida daga kauyen Samira.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa wasu sojojin sun jikkata.

Mayakan da ke ikirarin jihadi suna yawan kai hare-hare a yankin da ke kan iyaka da Burkina Faso.

Sojojin Nijar suna fuskanta hare-hare daga ‘yan ta’adda da suka hada da Boko Haram, da al-Qa’ida, da Islamic State.

Hare-haren na ci gaba duk da cewa manyan kasashe masu karfin soji, wato Faransa da Amurka suna tallafa wa kasar da kayan aiki.

MAJIYA:AFP