| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa
Za a dauki duk wata hukuma da aka gano tana bai wa ofishin jakadancin Faransa lantarki ko ruwa a matsayin “makiyiyar al’umma,” in ji rahotanni.
Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa
Hakan na faruwa ne a yayin da wa'adin da sojoji suka bai wa jakadan Faransa a Nijar na fita daga kasar ya wuce./Hoto:AA / Others

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun katse wutar lantarki da ruwa na ofishin jakadancin Faransa da ke kasar, sannan sun hana a kai abinci cikinsa, a cewar rahotanni da dama.

Sojojin sun dauki irin wannan mataki a karamin ofishin jakadancin Faransan da ke birnin Zinder, kamar yadda rahotanni suka bayyana ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin kasa da ke goyon bayan sojojin mai suna National Support Committee for the National Council for the Safeguarding of the Country (CNSP), Elh Issa Hassoumi Boureima, ya bukaci dukkan hukumomin da ke bayar da ruwa da wutar lantarki da abinci su daina bai wa ofishin jakadancin na Faransa, a cewar rahotanni.

Kazalika, duk hukumar da aka gano tana bai wa ofishin jakadancin Faransa wadannan abubuwa, za a dauke ta a matsayin “makiyiyar al’umma,” in ji rahotanni.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kori jakadan Faransa daga kasar

Rahotannin na zuwa ne bayan wa’adin da sojojin suka bai wa jakadan Faransa da ke kasar na awa 48 ya cika ranar Lahadi.

Sojojin na Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fice daga kasar cikin awa 48 a yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan jiya.

Nijar ta fada cikin rikici ranar 26 ga watan Yuli bayan Janar Abdourahamane Tiani, wani tsohon shugaban sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar, ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum.

Bayan nan ne Faransa da wasu kasashen Yamma suka soma kwashe 'ya'yansu daga Nijar.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile
Dubban mutane sun yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga sojin Nijar bayan dakile yunƙurin tawaye
Hatsarin mota a Masar ya yi ajalin mutum 16 a sanannen yanki mai cike da ‘yan yawon bude ido
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da boren da aka yi a Nijar
An kama ‘yar jarida mai yawan mabiya Denise Dusauchoy ‘yar kasar Kongo a Tanzania
Tebboune ya sake bayyana goyon bayan Aljeriya ga Nijar yayin da ake fuskantar barazanar tsaro
Yadda maganin rana guda zai iya kawo ƙarshen cutar bacci a Afirka
Mayaƙa 200 sun fice daga RSF ta Sudan inda suka sauya sheƙa zuwa rundunar sojin ƙasar
Ghana ta kama mabarata fiye 1,000 a Accra da Kumasi – Hukumar Shige ta Fice ta Ghana
Algeria ta aika jiragen yaƙi huɗu zuwa Jamhuriyar Niger bayan tashin hankali a Niamey
Sojin ruwan Turkiyya da dakarun Somaliya sun ceto jirgin dakon kaya daga 'yanfashin teku
Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro
’Yan a-waren azbinawa sun saki sojojin Mali 60 da suka sace
An ji karar harbe-harben bindiga a kusa da sansanin soji da kuma fadar shugaban kasa a Nijar
Traore ya buƙaci matasan Burkina da su guji bin 'ɓarauniyar hanya' wadda ke kaiwa ga cin amana
Sojojin Sudan sun yi ikirarin harbo wani jirgi maras matuƙi kusa da iyakar Habasha
Gwamnatin Ghana ta yi watsi da gudunmawar cedi miliyan 20 daga kamfanin MTN
Manufar Afirka ta shiga ofis mafi girma a MDD: Ko hakan ba zai iya sake faruwa ba?
Nijar ta cim ma yarjejeniyar gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai karfin MW 200
Gwamnatin Ghana za ta kawo ƙarshen binciken da ‘yansanda ke yi na ababen hawa a kan hanya