| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur ga ma'aikatun gwamnati
Shugaba Tinubu ya bayar da umarni kan a koma amfani da motoci masu amfani da gas inda ya ce a yi watsi da duk wata takarda wadda aka gabatar da ke buƙatar a sayi motoci masu amfani da fetur.
Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur ga ma'aikatun gwamnati
Matakin na Shugaba Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun wahalar man fetur a Nijeriya. / Hoto: DOlusegun/X / Others

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarni kan an haramta sayen motoci masu amfani da fetur a koma sayen masu amfani da gas ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Shugaban ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wanda aka gudanar a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelele ya fitar ta ce.

Shugaban ya ce ya bayar da wannan umarnin ne a yunƙurin ƙasar na komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli inda sanarwar ta ce an gano gas ɗin CNG ba ya fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli kamar fetur.

"Wannan ƙasar ba za ta samu ci gaba ba idan muka ci gaba rawa a wuri guda. Muna da burin aiwatar da amfani da CNG a faɗin ƙasa, kuma dole mu kafa misali da jami'an gwamnati domin su nuna hanyar makoma mai kyau ga mutanenmu. Hakan zai fara da mu, idan aka ga

Haka kuma shugaban ya bayar da umarni kan a yi watsi da duk wata takarda wadda aka gabatar a gaban Majalisar Zartarwar ta Tarayya wadda ke buƙatar a sayi motoci masu amfani da fetur.

Matakin na Shugaba Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun wahalar man fetur a Nijeriya.

A kwanakin baya ne gwamnmatin ta Tinubu ta cire tallafin man fetur a ƙasar, wandahakan ya sa farashin fetur ɗin ya ƙaru matuka a ƙasar.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Majalisar Dinkin Duniya ta amince a sake zana taswirar Afirka zuwa ainihin yadda nahiyar take
Nijar na zargin Faransa da tunzura sojojin da suka yi yunkurin tawayen da aka dakile
Tallafin ƙasashen waje da harin jiragen sama marasa matuƙa sun ƙara tsananta yaƙin Sudan - MDD
Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile
Dubban mutane sun yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga sojin Nijar bayan dakile yunƙurin tawaye
Hatsarin mota a Masar ya yi ajalin mutum 16 a sanannen yanki mai cike da ‘yan yawon bude ido
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da boren da aka yi a Nijar
An kama ‘yar jarida mai yawan mabiya Denise Dusauchoy ‘yar kasar Kongo a Tanzania
Tebboune ya sake bayyana goyon bayan Aljeriya ga Nijar yayin da ake fuskantar barazanar tsaro
Yadda maganin rana guda zai iya kawo ƙarshen cutar bacci a Afirka
Mayaƙa 200 sun fice daga RSF ta Sudan inda suka sauya sheƙa zuwa rundunar sojin ƙasar
Ghana ta kama mabarata fiye 1,000 a Accra da Kumasi – Hukumar Shige ta Fice ta Ghana
Algeria ta aika jiragen yaƙi huɗu zuwa Jamhuriyar Niger bayan tashin hankali a Niamey
Sojin ruwan Turkiyya da dakarun Somaliya sun ceto jirgin dakon kaya daga 'yanfashin teku
Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro
’Yan a-waren azbinawa sun saki sojojin Mali 60 da suka sace
An ji karar harbe-harben bindiga a kusa da sansanin soji da kuma fadar shugaban kasa a Nijar
Traore ya buƙaci matasan Burkina da su guji bin 'ɓarauniyar hanya' wadda ke kaiwa ga cin amana
Sojojin Sudan sun yi ikirarin harbo wani jirgi maras matuƙi kusa da iyakar Habasha
Gwamnatin Ghana ta yi watsi da gudunmawar cedi miliyan 20 daga kamfanin MTN