Mutum goma sha daya ne suka mutu a hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyuka biyu na Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da Burkina Faso a karshen mako, a cewar sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ranar Lahadi.
"’Yan ta’adda a kan babura da dama sun kai hari a kauyukan Amara da Loudji," masu nisan kilomita 30 a kudu maso gabashin Bankilare, "inda suka kashe mutum 11," in ji sanarwar.
Sun kai harin ne a yayin da jami’an tsaron Nijar suka “kaddamar da jerin hare-hare” ranar Juma’a, wadanda ma’aikatar tsaron ta ce “sun lalata daukacin” hanyoyin sadarwar ‘yan ta’addan.
Ta kara da cewa an kashe soja daya tare da jikkata guda biyar ranar Juma’a lokacin da motarsu da ke yin sintiri ta taka nakiya a kauyen Ouro Gueladjo, mai nisan kilomita 70 daga Yamai, babban birnin kasar.
Labari mai alaka: Nakiya ta kashe sojoji bakwai a Jamhuriyar Nijar
Tun daga watan Yuli sojoji suke mulki a Nijar bayan sun kifar da gwamnatin farar-hula.
Ranar 17 ga watan Disamba, shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce kasar tana "samun ci-gaba" wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa sojoji sun samu “nasarori da dama” ta hanyar dakile tarzoma.
Sojoji da mazauna yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali sun ce an samu kwanciyar hankula a makonnin da suka gabata.
A watan Oktoba an kashe sojoji shida a kan iyakar Nijar da Burkina Faso sakamakon ba-ta-kashi da ‘yan bindiga.
Kazalika a watan na Oktoba, an kashe sojojin Nijar 29 a hari mafi muni da ‘yan bindiga suka kai musu tun bayan juyin mulkin da soji suka yi.
















