| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
‘Yan uwan Bazoum ba su ji duriyarsa ba tun 18 ga watan Oktoba
Sojojin Nijar sun ki sakar Mohamed Bazoum duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya da kungiyoyi da dama suke ta yi.
‘Yan uwan Bazoum ba su ji duriyarsa ba tun 18 ga watan Oktoba
Sojoji na riƙe da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa a gidansa da ke fadar shugaban kasa tun da suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli. / Others

‘Yan uwan hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ranar Alhamis sun ce ba su ji labarin halin da yake ciki ba tun ranar 18 ga watan Oktoba, suna masu Allah wadai da yadda ake “kamawa da kuma gudanar da bincike” a kan wasunsu.

Sojoji na riƙe da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa a gidansa da ke fadar shugaban kasa tun da suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli.

Sojojin sun ƙi sakarsa duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama suke ta yi.

"Tun ranar 18 ga watan Oktoba, ba mu ji labarin halin da Shugaba Bazoum da matarsa Khadija Mabrouk da ɗansa Salem suke ciki ba a fadar shugaban ƙasa inda ake tsare da su," kamar yadda ‘yan'uwansa suka bayyana a wata sanarwa da suka fitar.

"Hukumomin soji sun kama wasu daga cikin danginmu da dama suna kuma bincike a kansu ta salon cusgunawa,” in ji sanarwar.

Lauyan zuri'ar, Ould Salem Said, ya shaida wa manema labarai cewa "mun lura da wani abu da ke faruwa a kan iyalan Shugaba Bazoum."

A ranar Talata ne aka bincike gidajen ɗaya daga cikin ƴayan ƴan'uwan Bazoum da na wani ɗan'uwan nasa a Yamai babban birnin ƙasar, a cewar Said.

Wani labari mai alaƙa: Juyin mulkin Nijar: Jagoran juyin mulkin da kasa cimma sulhu da kuma kalubalen dimokuradiyya

Lauyan ya ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani kawun Bazoum a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ƙara da cewa ya gabatar da koke ga ofishin mai shigar da ƙara na gwamnati kan “sacewa da ƙwace da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba".

Said ya kuma ce an kama ɗan’uwan matar Bazoum a kudancin ƙasar, kuma “an miƙa shi a hannun ‘yan sanda".

Tun a ranar 26 ga watan Yuli ne shugabannin sojojin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani ke mulkin Nijar.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai