Yadda bikin baje kolin fasahohin  Ghana ya haskaka yankin Volta
Bikin fasahar zane-zane na titunan Tsadidi yana mai da hankali ne kan bikin al'adu da fasashohin Ghana. / Hoto: Glenn Samm   / Others
Yadda bikin baje kolin fasahohin  Ghana ya haskaka yankin Volta
Bikin na kwanaki uku ya nuna al'adun gargajiyar Ghana kana ɓude taron bikin ne daga gabar tekun garin Keta, ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido a yankin Volta.
7 Nuwamba 2024

An gudanar da bikin baje kolin fasahohi na Ghana wanda ke mai da hankali kan bikin fasahar zane-zane da al'adu da kuma yawon buɗe ido a kwanan nan a yankin Volta na ƙasar.

Bikin na kwanaki uku, wanda aka gudanar daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba, an soma shi ne a ranar Juma'a da jawaban ilimantarwa ga daliban fasahar zane-zane na garin Keta da Alonga – manyan wuraren yawon buɗe ido biyu da ke yankin Voita a ƙasar.

Bikin fasahohi na Tsadidi, wanda a yanzu ya kai shekara uku da aka soma, yana nufin yawon shakatawa a harshen Ewe. Glenn Samm, wani mai ba da labari ta hanyar zane-zane kana mai tallan ƙawa ne ya ƙirkire bikin.

Kimanin masu yawon bude ido miliyan 1.1 ne suka ziyarci Ghana a shekarar 2023, a cewar wata kiɗiddiga da aka fitar.

Taken bikin Tsadidi na bana a shekarar 2024 shi ne, "Gwajin Al'adu," inda aka baje kolin kayayyakin tarihi na yankin Volta.

Wasannin al'adu

An ƙarkare bikin na ranar Juma'a ne da zaman shan ɗumin wuta da ba da tatsuniya, sannan aka ɗora da tattakin fasahar zagaye garin Keta a ranar Asabar.

An baje kayayyaki da tufafin gargajiya da zane-zanen fasahohi akan hanyoyi da dai sauran wasannin al'adu a muzaharar da aka yi.

Bikin ƙarshe da aka gudanar a ranar Lahadi, an yi ciye-ciye a bakin teku inda aka baza abincin gargajiya iri daban-daban tare da kiɗe-ƙiɗe na gargajiya.

Ayyukan nishaɗi

"Biki yana haɗa mutane wuri ɗaya da kuma masu ba da tallafi zuwa bikin bisa ga mabambantan dalilai, ciki har da shaida irin al'adun gargajiya da ake da su,'' kamar yadda Glemn Samm ya bayyana a wata hira da kafar Grapic Showbiz ya yi da shi.

“Kamar dai yadda aka saba, bikin baje kolin fasahar Tsadidi yana ƙirkirar ayyukan nishaɗi ga mahalarta kana a wannan karon da aka gudanar da bikin an samar da shirye-shiryen nishaɗi daban-daban, inda aka fi mai da hankali kan fasahohi,'' in ji shi.

Glenn Samm, wanda ainihin sunansa shi ne Samuel Glenn Semakor, ya lashe lambar yabo ta Fashion Influencer na shekara na shirin Pulse Influencer a shekarar 2022.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarin
Mohbad: Taƙaddama game da ko marigayi mawaƙin Nijeriya shi ne uban ɗansa na asali
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
Azumi da Ciwon Suga: Shawarwarin ƙwararrun Lafiya ga Musulmai a watan Ramadan
An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi
Cibiyar Al’adu ta Yunus Emre ta haɗa Turkiyya da Nijeriya ta hanyar fasaha
Yadda azumin Ramadan ke inganta lafiyar jiki
Dalilan da za su ba lallai a fara azumin Ramadan na 2026 ranar Laraba ba a Nijeriya
Dalilin da ya sa harshenku na asali ke tsara duk wani yare da kuke magana da shi
Dalilin da ya sa har yanzu kuturta ke cikin cututtukan da ke addaba da barazana ga ɗan'adam
Wa ke da alhakin cutuwar yara sakamakon amfani da kafafen sada zumunta na intanet?
Dalilin da ya sa faɗuwar jarrabawa watakila batun tsari ne ba na ɗalibi ba
Kunkuru Jonathan: Dabba mafi tsufa da ya kwashe shekaru 193 a duniya
Gaskiya mai ɗaci: Yadda rashin haraji mai yawa kan lemuka da giya ke illata lafiyar mutanen Afirka
Aden Abdullahi: Wani matashi da ke kula da dabbobin da ke gararamba a kan titi
Kenya na jimamin mutuwar toron giwa mai babban haure, da ya shekara 54 a duniya
Wani ɗan Nijeriya, Fado the Great yana ƙoƙarin maido da tashen wasan tsafi