| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Neymar yana samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa
Sai dai likitoci ba su bayyana takamaimai lokacin da dan wasan zai koma taka leda ba, amma ana iya kaiwa wata takwas zuwa 10 kafin a warke daga karaya ko tsagewar kashi.
Neymar yana samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa
Ana iya kaiwa wata takwas zuwa 10 kafin a warke daga tsagewar kashi ko karaya. / Hoto: AP / AP

Neymar ya soma samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa sai dai har yanzu likitoci bayyana takamaiman lokacin da dan wasan kungiyar Al-Hilal zai koma taka leda ba.

Dan wasan, mai shekaru 31, ya samu karaya da tsagewar kashi a sawun gwiwar kafarsa ta hagu a lokacin da yake taka leda wa Brazil a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 a watan jiya.

Ana iya kaiwa wata takwas zuwa 10 kafin a warke daga tsagewar kashi ko karaya.

Dokta Rodrigo Lasmar, likitan kungiyar kwallon kafa ta Brazil, ya ce Neymar na iya kokarinsa wajen ganin ya samu cikakkiyar lafiya.

"Tun da farko ya nuna jajircewarsa, wajen bin ka'idojn da muka shimfida masa," Lasmar ya shaida wa wani taron manema labarai a Sao Paulo a ranar Litinin.

An fitar da Neymar daga filin wasa cikin hawaye a kan gadon daukar marasa lafiya yayin wasa tsakanin kasarsa Brazil da Uruguay inda aka tashi da ci 2- 0.

Ya koma kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya a lokacin bazara daga Paris St-Germain a kan Yuro miliyan 90, sai dai tun daga lokacin wasanni biyar kawai ya iya buga wa kungiyar sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Masoyin Arsenal ɗan Uganda na barazanar kai Gunners kotu kan damuwar da ya shiga bayan shan kaye
Danwasan Ghana, Kudus ya samu rauni a Tottenham, zai iya gaza zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026
Anthony Joshua 'zai koma damben boksin' bayan mummunan hatsarin mota
Mbappe da Vinicius za su koma aiki tare a wasan Real Madrid da Bayern Munich
Ghana ta kori kocinta Addo makonni gabanin gasar cin kofin duniya
Ina Mo Salah zai koma daga Liverpool?
Nijeriya ta doke Iran a wasan sada zumunta da suka buga a Turkiyya
Lukaku ya ƙi komawa atisaye a Napoli bayan janyewa daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa
Batun kofin AFCON: Me zai faru da ƙwallon ƙafa a Afirka bayan tataɓurza kan Senegal?
'Yanwasan Super Eagles 21 sun isa birnin Antalya na Turkiyya don wasannin sada zumunta
Mbeumo da Sesko na Man United ba za su je buga wa kasashensu wasan sada zumunta ba
Senegal za ta daukaka ƙara kan hukuncin ƙwace mata Kofin AFCON 2025
Tsohon golan Manchester United, Sergio Romero, ya yi ritaya daga kwallo
Joan Laporta ya sake zama shugaban Barcelona bayan lashe zaɓe
Trump ya sa tawagogin kasashen Afirka cikin matsala a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026
Barcelona za ta ƙwato Haaland daga Manchester City don maye gurbin Lewandowski
Courtois ya jajanta wa golan Tottenham da aka ci ƙwallo 3 a minti 16 da fara wasa
Ƙwallon da Galatasaray ta zura a raga a farkon wasa ya nutsar da Liverpool a karawar Zakarun Turai