Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kara jaddada bukatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga kwamitin wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.
“Sakamakon watsi da Amurka ta yi da kudirin, ba a cimma wata matsaya ba. Yana da kyau a yi garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a wani jawabi da ya yi a ranar Asabar a taron Ranar Kare Hakkin Bil’adama ta Duniya wanda aka gudanar a birnin Santambul.
“Mun cire rai da yanke tsammani da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” in ji shi. “ Tun daga 7 ga watan Oktoba, kwamitin tsaron wanda aikinsa shi ne samar da zaman lafiya ya koma ba Isra’ila kariya.”
Isra’ila ta koma kai hare-hare ba kakkautawa kan Gaza tun daga 1 ga watan Disamba bayan an shafe mako guda ana morar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Falasdinu.
Kusan Falasdinawa 17,500 aka kashe a Gaza da aka yi wa kawanya a hare-hare ta sama da kasa tun bayan kaddamar da harin a ranar 7 ga watan Oktoba.
'Masu kashe mutane a Gaza za su girbi abin da suka shuka'
Erdogan ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila wadda ke samun cikakken goyon bayan Kasashen Yamma na gudanar da zalunci da kisan kiyashi a Gaza wanda ke kunyata bil’adama baki daya.
Ya kara jaddada cewa masu kashe mutane a Gaza za su girbi abin da suka shuka kan take hakkin bil adama da suka yi ko ba dade ko ba jima.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar samar da duniya mai adalci, sai dai ba tare da Amurka ba saboda tana tare da Isra’ila.
















