| Hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
'Za mu iya zama mai shiga tsakani a rikicin Gaza': Shugaba Erdogan
Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi tayi cewa kasarsa ta zama mai shiga tsakani a yakin da Isra'ila ke yi da Falasdinu, yana mai bayyana kwarin gwiwar samar da mafita a rikicin.
'Za mu iya zama mai shiga tsakani a rikicin Gaza': Shugaba Erdogan
Turkiyya na daga cikin kasashen da ke kan gaba wurin kai kayan agaji a Gaza wadda Isra'ila ke kai wa hari. Hoto/AA / AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya a shirye take domin zama mai shiga tsakani a rikicin da Isra’ila take yi da Falasdinu bayan ziyarar da ya kai Kazakhstan.

Erdogan ya jaddada irin karfin da Turkiyya ke da shi a matsayin kasa wadda za ta iya tabbatar da tsaro a Gaza, inda ya jaddada matakan tsaro, siyasa, tarihi, da al'adu.

Ya kara jaddada goyon bayan tsare-tsare wadanda za su samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da ya yi watsi da tsare-tsaren da ke kara tsananta wahalhalun da Falasdinawan ke ciki da kuma kara rura wutar rikicin da ake fama da shi.

Yayin da ya duba kan makomar Gaza, Erdogan ya bayyana fatan da ake da ita ga Gaza a matsayin yanki mai zaman lafiya kan iyakokin da aka shata mata a 1967, wanda ta hadu ta zama kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci wadda Gabashin Birnin Kudus zai kasance babban birnin.

Ya jaddada goyon baya kan tsarin da zai samar da zaman lafiya sannan ya yi watsi da tsarin da zai ta'azzara mawuyacin halin da Falasdinawa suke ciki.

Duniya da Tarayyar Turai sun bari ana kashe fararen-hula

Kasashen Duniya da Tarayyar Turai sun kawar da kai kan hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Gaza inda take lalata dukkan cibiyoyin kiwon lafiya, tare da bari ana kashe jarirai da fararen-hula, in ji Erdogan.

Ya zargi Tarayyar Turai da "daukar matakai masu ban mamaki da yin baki-biyu", sannan Erdogan ya kara da cewa Tarayyar Turai “ba ta gabatar da wani tsari na adalci ba kuma ba za ta iya gabatarwa ba.”

“Kun lura sosai da mutanen da ke goyon bayan Isra'ila a yanzu, da kuma wadanda ba su shiga tattaunawar diflomasiyya ba a rikicin Rasha da Ukraine? Tarayyar Turai ce,” in ji shugaban Turkiyya a hirarsa da manema labarai.

MAJIYA:TRT World