Faɗan 'yan daba a Haiti ya janyo tagayyarar yara sama da 300,000 tun watan Maris, kamar yadda Hukumar Yara da Majalisar Ɗinkin Duniya ta faɗa a ranar Talata, yayin da ƙasar da ke yankin Caribbean take fama da kashe-kashe da garkuwa da mutane.
Yara su ne sama da rabin mutane 580,000 da suka rasa gidajensu cikin watanni huɗu na bayan nan.
“Wannan bala'in yana faruwa ne a kan idonmu, kuma yana haifar da mummunan tasiri ga yara,” cewar Catherine Russell, babbar daraktar UNICEF cikin wata sanarwa.
“Yaran da suka tagayyara suna cikin matsanancin buƙatar yanayi mai aminci da tsaro, kuma da ƙarin tallafi da kuɗaɗe daga ƙasashen duniya.”
A yanzu gungun 'yan daba suna iko da aƙalla kashi 80% na babban birnin ƙasar Port-au- Prince da kuma muhimman hanyoyin da ake shiga da fita daga birnin, sannan an kashe ko jikkata fiye da mutum 2,500 a faɗin ƙasar a watannin ukun farko na shekarar, a cewar MDD.
Yara da dama suna zaune a sansanoni marasa tsafta, ciki har da makarantu, lamarin da ke sanya su cikin barazanar kamuwa da cuta. RUfe makarantu ma ya jawo an samu raguwar yara da yawa da suka daina zuwa makaranta.
Hukumar ta ce ana tilasta wa yara a Haiti shiga cikin gungun 'yan daba don su rayu, saboda ba sa samun abinci da harkar lafiya da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli.
Kazalika yaran na fuskantar cin zarafi da fyaɗe da azabtar da su da raba su da iyalansu, in ji UNICEF.
Sanarwar na zuwa ne bayan da ɗaruruwan jami'an tsaron Kenya suka isa Haiti don taimakawa wajen ceton ƙasar daga bala'in da 'yan daba suka saka ta a ciki.
Zuwan jami'an tsaron ya sa an samu mabambantan ra'ayoyi bayan da a shekarun baya tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta kai cutar kwalara ƙasar sannan aka yi mata zarge-zargen cin zarafi.
A ranar Litinin ne, Mataimakin Mai Bai wa Shugaban Tsaro na Amurka Shawara, Jonathan Finer ya gana da Firaministan Haiti Garry Conille don tattaunawa kan tawagar farko da aka tura Haiti wadda ke samun goyon bayan MDD.
Finer ya tunatar da Conille game da ƙaƙƙarfan goyon bayan Amurka ga tabbatar da sa ido a matsayin wani ɓangare na manufar.