Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, reshen Al Qassam Brigades, ta sanar da cewa, ta kashe sojojin Isra'ila 12 a yankin arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya.
"A wani gagarumin farmaki da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Zirin Gaza, mayakan Al-Qassam sun kai hari kan wata buldozar soji ta sojan Isra'ila D9 da harsashin Yassin 105 tare da kai hari kan dakaru masu tsananin aƙidar son kafa ƙasar [Isra'ila] da suka kutsa cikin wani gida dauke suka yi fito na fito da su, ”in ji sanarwar a ranar Laraba.
“Isar jami’an ceto wajen ke da wuya sai aka tayar da bama-bamai a kan wata tankar Merkava, kuma bayan yunkurin kwato na’urorin sojojin da aka jibge a kasa, sojojin saman Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a yankin ba tare da tausayi ba, sannan mayakanmu sun yi ta luguden wuta. Ya tabbatar da kashe sojojin Isra'ila akalla 12 a farmakin," in ji sanarwar.
Tun da farko a ranar Larabar da ta gabata ce sojojin Isra'ila suka sanar da cewa, sun kaddamar da wani gagarumin farmakin soji a tsakiyar sansanin Jabalia, a daidai lokacin da ake ci gaba da kai wani farmaki a gabashin birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Ta ce a harin da aka kai a Jabalia, an yi ta gwabza kazamin fadace-fadace, wanda ke nuni da cewa dakarunta "sun yi arangama da tarin mayaƙa," wanda ke nufin wasu ɓangarorin Falasdinawa.













