| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Hannayen-jarin kamfanonin Faransa sun fadi bayan juyin mulki a Gabon
Hannayen-jarin kamfanonin Maurel & Prom, Eramet, da reshen TotalEnergies na kasar Gabon sun fadi da kashi 15 zuwa 20, a cewar jaridar Les Echos da ake wallafawa a kowace rana a Faransa.
Hannayen-jarin kamfanonin Faransa sun fadi bayan juyin mulki a Gabon
Faransa ta ce tana sanya ido sosai a kan halin da ake ciki a Gabon. / Hoto: Reuters / Reuters

Hannayen-jarin kamfanonin Faransa uku sun fadi a kasuwar hada-hadar hannun-jari ta Paris ranar Laraba bayan sojoji sun sanar da kifar da gwamnati a Gabon, inda suke gudanar da harkokinsu.

Hannayen-jarin kamfanonin Maurel & Prom, Eramet, da reshen TotalEnergies na kasar Gabon sun fadi da kashi 15 zuwa 20, a cewar jaridar Les Echos da ake wallafawa a kowace rana a Faransa.

Tun da farko kamfanin hakar ma'adinai na Eramet ya sanar cewa ya dakatar da ayyukansa da kuma sufurin jiragen kasa a Gabon.

Labari mai alaka: Ali Bongo Ondimba ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar Gabon

Wasu manyan sojojin Gabon sun bayyana a gian talabijin da sanyin safiyar Laraba inda suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo.

Sanarwar tasu na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta ayyana Shugaba Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben karo na uku indaya samu kashi 64.27 na kuri'un da aka kada.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Damuwar 'yan Republican na ƙaruwa gabanin zaɓukan rabin wa'adi saboda tasirin yaƙin Iran
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran