Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe Falasɗinawa da dama a Khan Younis. / Hoto: AA

Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024

1309 GMT — Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe Falasɗinawa da dama a Khan Younis

Hukumomin asibiti sun ce wasu hare-hare biyu da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe akalla mutane takwas a garin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Harin farko ya afku ne a wani gida a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke yammacin birnin, inda ya kashe mutum uku a cewar asibitin Nasser, inda aka kai gawarwakin mutanen.

Harin na biyu ya afka wa tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Absa da ke gabashin Khan Younis, inda ya kashe biyar.

1332 GMT — Shugaban Iran ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa yin shiru ba yayin da ake ƙoƙarin far mata

Kasar Iran ba za ta taba yin shiru ba wajen fuskantar cin zarafi ga muradunta da tsaronta, Shugaba Masoud Pezeshkian ya shaida wa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin bayan kisan da aka yi a Tehran a makon jiya na shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh. .

1004 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin Isra'ila a Gaza sun kai 39,677

Sojojin Isra'ila sun sake kashe Falasɗinawa 24 a hare-haren da suka kai a faɗin Gaza, lamarin da ya sa yawan mutanen da suka mutu tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu ya kai 39,677, a cewar Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ƙara da cewa zuwa yanzu kuma mutum 91,645 ne suka jikkata.

"Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 24 tare da jikkata wasu 110 a "kisan kiyashi biyu' da aka yi wa iyalai da dama a cikin awa 24," in ji ma'aikatar. Ta ƙara da cewa "har yanzu akwai mutane da dama da ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzai saboda masu aikin ceto sun gaza ciro su."

0652 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta bayar da sabon umarni ga Falasɗinawan da ke arewacin Gaza su fice daga yankin wanda aka kwashe watanni 10 ana yi wa luguden wuta.

Rundunar sojin ta ce za ta mayar da martani ga harin rokokin da Hamas ta harba mata daga yankin Beit Hanoon inda ta umarci mazauna yankin su fice zuwa Birnin Gaza, wani babban yanki da aka riga aka rusa.

Beit Hanoon, wanda ke kan iyaka, na cikin wurare na farko da dakarun Isra'ila suka riƙa yi wa luguden wuta babu ƙaƙƙautawa tun da suka ƙaddamar da hare-hare bayan kutsen da ƙungiyar Hamas ta yi a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Dakarun Isra'ila suna yawan komawa yankunan da suka lalata ta hanyar yi musu luguden wuta.

Isra'ila ta raba galibin al'ummomin Gaza miliyan 2.3 da gidajensu tun lokacin da ta soma kai hare-hare a yankin.

Dubbansu suna samun mafaka a tantuna da ke cike da jama'a.

2038 GMT — Hezbollah ta yi murna da naɗin Sinwar a matsayin sabon shugaban siyasa na Hamas

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta taya murna ga Yahya Sinwar bayan naɗinsa a matsayin sabon shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, tana mai cewa matakin ya nuna cewa burin Isra'ila na kashe Ismail Haniyeh bai cika ba.

Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren siyasa na Hamas kuma jagora a tattaunawar neman tsagaita a Gaza, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a gidansa da ke Tehran ranar 31 ga watan Yuli jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran.

Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kisan Haniyeh da gwamnatin Netanyahu ta yi.

Zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban Hamas "ya aike da babban saƙo ga masu mamaya (Isra'ila) cewa Hamas za ta ci gaba da gwagwarmaya", a cewar wai sabban jami'in Hamas a hira da kamfanin labarai na AFP.

Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren siyasa na Hamas kuma jagora a tattaunawar neman tsagaita a Gaza, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a gidansa da ke Tehran ranar 31 ga watan Yuli jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran. / Hoto: Reuters
TRT Afrika da abokan hulda