Falasɗinawa suna yin hijira zuwa yankin Al Mawasi bayan Isra'ila ta ba su umarni su fita daga yankin Hamad na birnin Khan Yunis da ke Gaza ranar 11 ga watan Agusta, 2024. /Hoto: Reuters

Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024

1206 GMT –– Harin da jiragen saman Isra'ila suka kai a kudancin Lebanon ya jikkata mutum uku

Akalla mutum uku ne suka jikkata sakamakon wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a kudancin kasar Lebanon, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana a yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali tsakanin Isra'ila da Hizbullah.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce an kai harin na dare ne a garin Kfar Kila.

An kuma bayar da rahoton wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a garuruwan Chihine da Borj El Mlouk, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya rawaito cewa, an kai hare-haren sama kan tankokin yaki guda hudu a Ayta al Shaab a kudancin kasar Lebanon. Har yanzu babu wani bayani game da adadin wadanda suka ji raunuka ko barna da aka samu.

Aƙalla Falasɗinawa 142 Isra’ila ta kashe a wasu sabbin hare-hare da ta kai Zirin Gaza, wanda hakan ya kawo adadin Falasɗinawan da Isra’ilar ta kashe zuwa 39,897 tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda ma’aikatar lafiya da ke Gaza ta tabbatar da ranar Litinin.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa akwai wasu mutum 92,152 da suka jikkata tun bayan soma wannan yaƙin.

A sabon harin da Isra’ilar ta kai, ta bayyana cewa har yanzu akwai mutane da dama da ke ɓaraguzai suka danne bayan harin da Isra’ila ta kai.

0400 GMT — Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani su aiwatar da shirin Shugaban Amurka Joe Biden na tsagaita wuta a Gaza maimakokin gudanar da tarukan tattaunawa, a yayin da dubban Falasɗinawa suke ci gara da ficewa daga Khan Younis bayan Isra'ila ta ba su umarnin barin yankin.

Ƙungiyar ta yi kiran a yayin da Falasɗinawa suke ci gaba da ficewa aga yankin na Al Jalaa na Khan Younis wanda a baya Isra'ila ta ayyana a matsayin "tudun-mun-tsira".

Hamas ta ce tana so a aiwatar da shirin Biden na tsagaita wuta wanda ya gabatar ranar 31 ga watan Mayu sannan Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shil, "maimakon sake sabuwar tattaunwa".

A yayin da yake gabatar da shirin, Biden ya ce yana so a aiwatar da shi a matakai uku waɗanda za su kasance "wata hanya ta samun dawwamammen zaman lafiya da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su", kuma ya ce shiri ne na Isra'ila da kanta. Duk da wannan shawara, har yanzu an gaza aiwatar da matakin.

0104 GMT —Amurka ta tura jiragen yaƙi samfurin F-35 da jiragen ruwa zuwa Gabas ta Tsakiya

Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa mai ɗauke da makamai masu linzami zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon.

A tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, Austin ya jaddada aniyar Amurka ta ɗaukar "kowane irin mataki" domin kare Isra'ila, in ji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.

"Domin jaddada wannan matsayi, Sakatare Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa mai suna USS ABRAHAM LINCOLN, mai ɗauke da jiragen yaƙi samfuran F-35C, domin hanzarta isa cibiyar bayar da umarni, baya ga matakin da aka ɗauka na tura jirgin ruwa na USS THEODORE ROOSEVELT tun da farko," a cewar sanarwar.

Bugu da ƙari, Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa na USS Georgia (SSGN 729) mai ɗauke da makamai masu linzami zuwa cibiyar bayar da umarnin soji da ke yankin.

Kazalika jami'an tsaron sun tattauna kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da kuma muhimmanci rage kashe fararen-hula, da ci gaban da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, da kuma yunƙurin Amurka na "hana" Iran da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da sauran ƙungiyoyi da ke goyon bayan Iran kai hare-hare, a cewa Pentagon.

Amurka ta ce tana ƙokarin ganin an rage kashe fararen-hula da kuma hana Iran mayar da martani. / Hoto: Reuters Archive
TRT Afrika da abokan hulda