| Hausa
DUNIYA
5 MINTI KARATU
Isra'ila ta tabbatar da cewa mayakan Houthi sun kwace jirgin ruwa
Wannan shafin ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Isra'ila ta tabbatar da cewa mayakan Houthi sun kwace jirgin ruwa
Mayakan Houthi sun gargadi kasashe kan su janye jama'arsu daga jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila. / Hoto:Getty Images / Others

1600 GMT — Isra'ila ta tabbatar da cewa mayakan Houthi sun kwace jirgin ruwa

Isra’ila a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa mayakan Houthi sun kwace wani babban jirgin ruwa na daukar kaya.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra'ila.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar tsaro ta Isra’ila Daniel Hagari ya wallafa a shafin X, ya ce mayakan sun kwace jirgin ne a kusa da Yemen sai dai ya ce ba na Isra’ila bane.

1325 GMT — Hezbollah da Isra'ila na musayar wuta

An ji karar jiniyar gama-gari a birane da dama na Isra’ila da ke kusa da iyakar Lebanon a ranar Lahadi a daidai lokacin da kungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila ke harba wa juna rokoki.

Rundunar sojin Isra’ila a wata sanarwa ta bayyana cewa ta gano an harba rokoki goma daga Lebanon wadanda ke tafe zuwa garin Shlomi a kusa da iyakar da ke arewa.

Sai dai kafar watsa labarai ta Channel 12 ta ruwaito cewa babu wanda ya mutu ko kuma wata asara da aka yi.

1150 GMT — Mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra'ila

Mai magana da yawun kungiyar Houthi ta Yemen, Yahya Sarea ya bayyana cewa kungiyar za ta kai hari ga duk wani jirgin ruwa na kamfanonin Isra’ila ko kuma yake dauke da tutar ta Isra’ila, kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Telegram.

Yahya Sarea ya bukaci duka kasashen duniya su janye mutanensu da ke aiki a ire-iren jiragen ruwan.

Mayakan na Houthi sun yi wannan barazanar ne a daidai lokacin da adadin mutanen da Isra’ilar ta kashe ya haura 13,300 wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata.

0950 GMT— Dakarun Hamas sun ce sun kashe sojojin Isra'ila shida

Dakarun Al-Qassam Brigades na Hamas sun ce sun kashe sojojin Isra’ila shida a unguwar Juhor ad-Dik da ke kudu maso gabashin Gaza.

A wata sanarwa da suka fitar a ranar Lahadi, sun ce sun soma harba musu makamin roka, sai daga baya suka bi su da harbi da bindiga mai sarrafa kanta.

Zuwa yanzu babu wani karin bayani daga sojojin na Isra’ila kan sanarwar da mayakan na Hamas suka fitar.

0930 GMT— An sake kashe sojin Isra'ila biyu a Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa an sake kashe sojojinta guda biyu a Gaza, wanda hakan ya sa adadin sojin Isra’ilar da aka kashe ya kai 59 tun bayan da Isra’ilar ta kaddamar da kai hare-hare ta kasa a cikin Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba.

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce akwai karin sojan Isra’ilar daya da ya samu mummunan rauni a yayin da yake yaki a cikin Falasdinu.

Zuwa yanzu sama da mutum 12,300 Isra'ilar ta kashe a Gaza a hare-haren da take ci gaba da kaiwa ba kakkautawa.

0910 GMT — Isra'ila ta kashe mutane da dama a harin da ta kai Khan Younis

Akalla Falasdinawa 15 Isra’ila ta kashe a harin da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce jiragen yakin Isra’la sun kai harin ne da asubahi a gidaje biyu da ke Khan Younis.

Kamfanin dillancin labaran ya kara da cewa an kashe farar hula 13 a lokacin da jirgin ya kai hari kan gidan iyalan Zuhd da ke sansanin Nuseirat sannan wata mace da danta suka rasu a wani hari da jirgin sojin ya kai a gidan iyalan Abu Akar.

MAJIYA:AA, AFP, Reuters, AP, TRT World
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov