| Hausa
DUNIYA
7 MINTI KARATU
Turkiyya da Iraƙi sun tattauna kan cin zalin da Isra'ila ke yi a Gaza - Erdogan
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 199 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,097 tare da jikkata mutum sama da 76,980 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara.
Turkiyya da Iraƙi sun tattauna kan cin zalin da Isra'ila ke yi a Gaza - Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, ya tattauna da shugaban kasar Iraƙi kan zaluncin da Isra'ila ke yi a Falasdinu. Hoto: AA / Photo: Reuters / Reuters

1412 GMT –– Turkiyya da Iraƙi sun tattauna kan cin zalin da Isra'ila ke yi a Gaza - Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, ya tattauna da shugaban kasar Iraƙi kan zaluncin da Isra'ila ke yi a Falasdinu.

“Da takwarorina, mun tattauna kan illar zaluncin da Isra’ila ke yi a Falasdinu a yankinmu, kuma mun yi shawarwari kan matakan hadin gwiwa da za mu iya dauka,” in ji Erdogan a wani taron manema labarai.

Erdogan ya isa Baghdad babban birnin kasar Iraki domin ganawa da jami'an kasar. A ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Iraƙi, da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na duniya, da kokarin yaki da ta'addanci.

1232 GMT ––An tono gawawwaki fiye da 280 daga wani ƙaton kabari a Khan Younis

Ma'aikatan lafiya sun tono aƙalla gawa 283 daga cikin wani ƙaton kabari a Asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis na kudancin Gaza, a cewar rundunar sa-kai ta yankin.

"Ma'aikatan sa-kai sun tono ƙarin gawa 73 daga ƙaton kabari, abin da ya kai adadin gawawwakin da aka tono zuwa 283 tun daga ranar Asabar," in ji sanarwar da rundunar sa-kai ta fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ƴan sa-kai suna ci gaba da neman gawawwaki a kabarin.

An gano ƙaton kabarin ne ranar Asabar a harabar asibitin bayan dakarun Isra'ila sun janye daga cikinsa ranar 7 ga watan Afrilu inda suka kashe wata huɗu suna ɓarna.

"Mun yi amannar cewa akwai ƙarin ɗaruruwan da har yanzu ba a gansu ba waɗanda dakarun Isra'ila suka kashe su kuma suka binne su a manyan ƙaburbura,'' kamar yadda wani jami'in asibiti ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

0622 GMT — Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira a Gaza

Falasɗinawa da dama sun mutu kana wasu sun jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira da ke tsakiya da kudancin a Gaza.

Dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a sansanin ƴan gudun hijira na al Maghazi da ke gabashin Gaza da kuma kudu maso gabashin Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasɗinu ya ruwaito.

Isra'ila ta kashe tare da jikkata fararen-hula a hari ta sama da ta kai Masallacin al Taqwa da ke cikin sansanin ƴan gudun hijira na al Bureij a tsakiyar Gaza.

Kazalika jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a ƙofar shiga sansanin ƴan gudun hijira na al Bureij da kuma sansanin ƴan gudun hijira na al Nuseirat.

Haka kuma Falasɗinawa da dama sun jikkata bayan Isra'ila ta buɗe wuta a kusa da maƙabartar al Sawarha da ke sansanin al Nuseirat da kuma wani gida da ke unguwar al Burouk da yankin Deir al Balah na tsakiyar Gaza.

0130 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 24 a sabon harin da ta kai Rafah, galibinsu ƙananan yara ne

Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a hare-haren da jiragen samanta suka kai a wasu gidaje biyu a Rafah da ke kudancin Gaza ya ƙaru zuwa mutum 24, da suka haɗa da ƙananan yara 16 da mata shida, kamar yadda majiyoyi daga asibiti suka shaida wa Anadolu Agency.

Majiyoyin sun ce da dama daga cikin Falasɗinawan sun mutu ne sakamakon munanan raunuka da suka samu lokacin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai musu hari ranar Asabar a gabashi da tsakiyar Rafah.

Sun ce har yanzu akwai sauran mutane da ɓaraguzan gine-gine suka danne.

Ranar Asabar da maraice, rundunar ƴan sa-kai ta Gaza ta sanar da gano da dama daga cikin mutanen da aka kai wa hari a cikin gidajensu da ke gabashin Rafah.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ma'aikanta sun gano mutanen da "jirgin dakarun mamaya ya kai wa hari a wani gini mai hawa da yawa na iyalan Abdul-Aal da ke kan Titin George a gabashin Rafah.”

Kazalika ma'aikatan sa-kai "suna ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mutanen da suka ɓata.”

Lamarin ya faru ne a yayin da dakarun Isra'ila suke barazanar kutsawa cikin Rafah duk da gargaɗin da ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya suke yi, ganin cewa birnin shi ne wuri mafi girma da ƴan gudun hijira daga Gaza suke samun mafaka.

0005 GMT — Masar da MDD sun jaddada kira ga Isra'ila ta kawo ƙarshen 'cin zarafin' fararen-hula a Gaza

Masar da Majalisar Ɗinkin Duniya sun jaddada kira ga Isra'ila ta kawo ƙarshen "keta hakkin ɗan'adam" da take yi a kan fararen-hula da ke Gaza, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Masar ya bayyana ranar Lahadi.

Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry ya gana da wakiliya ta musamman na MDD, Francesca Albanese, game da halin da ake ciki kan kare hakkin ɗan'adam a yankin Falasɗinu a Alkahira a wani ɓangare na balaguron da zai kai ta ƙasashen da suka haɗa da Jordan.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar Ahmed Abu Zeid ya ce Shoukry da Albanese sun “jaddada kira ga Isra'ila don ta daina keta haƙƙoƙin ɗan'adam a Gaza, ta kuma bari a shigar da isassun kayan agaji da kuma hana Isra'ilawa ƴan-kama-wuri-zauna mamayar Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.”

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Guterres na MƊD ya yaba wa yadda Turkiyya ta shirya taron COP31
Amurka ta kwashe jiragen soji daga sansanin sama na biyu a Birtaniya bayan rahoton barazanar Iran
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Shin Turai za ta kare ICC, ko kuwa za ta ci gaba da neman yardar Amurka?
Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto
Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine
Hukumomin Faransa sun kama mutum 135 da ƙara dokar hana fita a wasu birane saboda zanga-zanga
Ba makawar yin Yaƙin Duniya na III in ji tsohon shugaban Serbia
Rubio ya ce taron shugabannin Amurka, Rasha da China zai amfani duniya sosai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari