Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024
1242 GMT — Harin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Zirin Gaza ya kashe Falasdinawa da dama
Akalla Falasdinawa bakwai ne aka kashe a sabbin hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai a Gaza, a cewar majiyoyin lafiya.
Dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta kan wasu fararen hula a unguwar Tel al-Hawa da ke birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum hudu, in ji kakakin hukumar tsaron fararen hula Mahmoud Basal a wata sanarwa da ya fitar.
Majiyoyin lafiya sun ce an kashe ƙarin mutane biyu a wani harin da aka kai kan babur da kuma taron fararen hula a kusa da wurin shakatawa na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza.
Wata majiyar lafiya ta ce, an kuma kashe wata Bafalasdiniya tare da jikkata wasu da dama a wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a tsakiyar Gaza.
0558 GMT —Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta ce ta ƙaddamar da hari da jirgi mara matuƙi a arewacin Isra'ila wanda rundunar sojin Isra'ila ta ce ya ya jikkata sojoji biyu tare da tayar da gobara.
Hakan na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar a yankin sakamakon kisan da Isra'ila ta yi wa kwamandan Hezbollah a Lebanon da kuma shugaban Hamas a Iran.
Wata sanarwa da Hezbollah ta fitar ta ce ta kai hari a sansanin sojojin Isra'ila da ke arewacin ƙasar a matsayin martani kan "hare-hare da kisan gillar" da sojojin Isra'ila suka yi a ƙauyua da dama a kudancin Lebanon.
Harin bai yi kama da wanda ake sa ran Hezbollah za ta kai ba don yin ramuwa kan kisan kwamandanta Fouad Shukur a Beirut a makon jiya.
Rundunar sojin Isra''ila ta ce ma'aikatan kwana-kwana suna aiki tuƙuru domin kashe gobarar da ta tashi sakamakon harin da ƙungiyar ta kai a yankin Ayelet HaShahar da ke Galilee.
0016 GMT — Netanyahu ya bijiro da sabbin sharuɗɗa kan musayar fursunoni a Gaza
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito da sabbin sharuɗɗa a wanda ya ce dole a cika kafin ya amince da yarjejeniyar musayar fursunoni da ƙungiyar Hamas, ciki har da tursasa wa Falasɗinawa kusan 150 barin ƙasarsu har abada, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar.
Ya ce dole ne a fitar da wasu Falasɗinawa daga ƙasarsu zuwa wasu ƙasashe bayan an sake su daga gidajen yarin Isra'ila, kamar yadda gidan talbijin na Channel 13 da ke Isra'ila ya ruwaito, inda ya ambato wasu majiyoyi da bai bayyana su ba.
A cewar majiyoyin, fursunonin, waɗanda suka kusa 150, ana zarginsu da kashe Isra'ilawa.
0205 GMT — Shugabannin tsaron Amurka da na Isra'ila sun tattauna kan matakin Washington na tura kayan yaƙi Gabas ta Tsakiya
Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin da takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant sun tattauna kan tura kayan yaƙi zuwa Gabas ta Tsakiya a wayar tarho da suka yi ranar Lahadi.
"Sun tattauna kan matsayin dakarun Amurka da matakin da Ma'aikatar Tsaro ta ɗauka na tura ƙarin matakan tsaro domin goyin bayan Isra'ila, da kuma yunƙurin hana ci gaba da tashin jijiyoyin wuya a yankin," in ji wata sanarwa da ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta fitar.
Yayin tattaunawar tasu, Austin ya jaddada goyon bayan da Amurka take bai wa Isra'ila na kare ta "a kowane hali" da kuma 'yancin Isra'ila na mayar da martani kan barazana daga Iran, da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da mayaƙan Houthi da ke Yemen.