| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Hamas ta ce jawabin Biden 'amincewa ce' ga Isra'ila kan ta ci gaba da yaƙin Gaza
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 319, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,139 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,743, kana an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzan gine-gine da aka rusa.
Hamas ta ce jawabin Biden 'amincewa ce' ga Isra'ila kan ta ci gaba da yaƙin Gaza
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya fito daga cikin mota a Tel Aviv yayin da zai tafi Masar ranar 20 ga Agustan 2024. / Hoto: Reuters / Photo: AFP / AFP

Talata, 20 ga watan Agusta, 2024

Kungiyar Hamas ta soki ikirarin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi na cewa ya janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza, tana mai kiran kalaman nasa a matsayin "amince wa" Isra'ila ta ci gaba da yakin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, Hamas ta bayyana cewa "kalaman wadanda ba su dace ba... ba sa nuna hakikanin matsayin kungiyar ba wacce ke da sha'awar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba", inda ta kira kalaman Biden a matsayin "amincewar Amurka ga gwamnatin Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi da ta ci gaba da aikata miyagun laifuka a kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba.

Biden, yayin da yake amsa tambayoyi kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Litinin, ya ce: "Isra'ila ta ce za su iya daidaitawa, a shirye suke. Amma an gaya min a yanzu Hamas tana ja da baya."

Hamas said Biden's statements do not reflect the true position of the movement, which has been keen to reach a cessation of hostilities.

Yayin da yake hawa jirgin sama bayan da ya yi jawabi a babban taron jam'iyyar Democrat a Chicago, ya kara da cewa: "Za mu ci gaba da ƙoƙari."

Hamas ta ce kalaman na Biden ba su yi nuni da hakikanin matsayin kungiyar ba, wanda ke da sha'awar cimma tsagaita wuta.

1245 GMT — Falasdinawa 12 sun mutu a harin da Isra'ila ta kai wata makaranta da suke samun mafaka

Rundunar tsaron farar hula ta Falasdinu ta ce harin da Isra'ila ta kai kan wata makarantar boko ya kashe akalla mutum 12, yayin da sojojin Isra'ila suka yi ikirarin kai hari a cibiyar kwamandojin Hamas.

Mai magana da yawun hukumar Mahmud Bassal ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, "ma'aikatanmu sun kwaso shahidai 12 daga Makarantar Mustafa Hafiz, da Isra'ila ta kai musu hari a yammacin birnin Gaza.

A baya dai Bassal ya bayar da adadin mutuwar mutum bakwai da jikkata wasu 15 a yajin aikin da ya ce ya afka wa hawa na biyu na ginin makarantar.

0717 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta gano gawawwaki shida na mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin ba-zata da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata ta ce ta gano gawawwakin ne a wani samame da ta kai da tsakar dare a kudancin Gaza.

Rundunar sojojin Isra'ila ba ta faɗi yadda aka kashe mutanen ba. Amma sau da dama Hamas ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe wasu daga cikin waɗanda ta yi garkuwa da su a luguden wutar ta take yi babu ƙaƙƙautawa a yankin, wanda ya mayar da kusan ɗaukacin yankin tamkar kufayi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 40,000 sakamakon hare-haren da take kai wa Gaza.

"Galibin mutanen da ta kashe mata da yara ne. Wannan babban bala'in ya faru ne sakamakon gazawar Rundunar Tsaron Isra'ila wajen kiyaye dokokin yaƙi," a cewar Babban Jami'i na MDD kan Kare Hakkin Ɗan'adam Volker Türk a wata sanarwa da ya fitar a baya bayan nan.

2033 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a Gaza a yayin da Amurka ke jan-ƙafa kan tattaunawar tsagaita wuta

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla tara, cikinsu har da yara, a wani hari ta sama da ta kai kan wani dandazn jama'a a sansanin al-Shati (Beach) da ke yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA.

"Jiragen yaƙin masu mamaya sun kai hari a wani rukunin gidaje da ke Khan Younis a kudancin Gaza," in ji kamfanin dillancin labaran.

2000 GMT — Hamas ta ce Amurka na jan-kafa kan tattaunawar tsagaita wuta don Isra'ila ta ci gaba da kisan kiyashi

Mai magana da yawun ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas Osama Hamdan ya ce ƙungiyarsu za ta yi biyayya ga shirin tsagaita wuta da a baya shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar, yana mai ƙarawa da cewa Washington na jan-ƙafa kan batun domin bai wa gwamnatin Netanyahu damar ci gaba da yin kisan kiyashi a Gaza.

Amurka tana "jan-ƙafa ne domin Israi'ila ta ci gaba da kisan kiyashin da take yi," kamar yadda Hamdan ya shaida wa Al Jazeera bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi iƙirari cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar masa zai goyi bayan shirin Amurka na tsagaita wuta a Gaza.

"Isra'ilawa sun janye daga shirin da Biden ya gabatar. Kalaman da Netanyahu ya yi game da amincewa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta sun nuna cewa Amurka ta gaza rarrashinsa domin ya amince da shirin da suka gabatar a baya," in ji Hamdan.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Guterres na MƊD ya yaba wa yadda Turkiyya ta shirya taron COP31
Amurka ta kwashe jiragen soji daga sansanin sama na biyu a Birtaniya bayan rahoton barazanar Iran
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Shin Turai za ta kare ICC, ko kuwa za ta ci gaba da neman yardar Amurka?
Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto
Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine
Hukumomin Faransa sun kama mutum 135 da ƙara dokar hana fita a wasu birane saboda zanga-zanga
Ba makawar yin Yaƙin Duniya na III in ji tsohon shugaban Serbia
Rubio ya ce taron shugabannin Amurka, Rasha da China zai amfani duniya sosai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari