| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Harin sama da aka kai a tsakiyar kasar Lebanon ba zai tafi a banza ba - Hezbollah
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 143 - ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 29,692, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 69,879.
Harin sama da aka kai a tsakiyar kasar Lebanon ba zai tafi a banza ba - Hezbollah
Wani ɗan majalisar dokokin Hizbullah ya ce harin da Isra'ila ta kai ta sama a Baalbek da ke tsakiyar kasar Lebanon "ba zai tafi a banza ba." / Hoto: Reuters / Photo: AFP / AFP

1338 GMT — Harin sama da aka kai a tsakiyar kasar Lebanon ba zai tafi a banza ba - Hezbollah

Wani ɗan majalisar dokokin Hizbullah ya ce harin da Isra'ila ta kai ta sama a Baalbek da ke tsakiyar kasar Lebanon "ba zai tafi a banza ba."

Hasan Fadlallah a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, maƙiya sun yi wa ƙasar Labanon barazana, kuma muna gaya musu cewa haƙurinmu na ƙarewa kuma za mu durfafi duk wani hari da za a kai wa ƙasarmu.

Dan majalisar na Lebanon ya sha alwashin cewa: "Wannan za a kawo karshen yaƙin cike da nasara."

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a Baalbek, lamarin da ke nuni da cewa lamarin na ta'zzara daga arangamar da ake samu a kan iyaka da ƙungiyar Hizbullah, kamar yadda shaidu suka shaida wa Anadolu. Ana kallon Baalbek a matsayin tungar Hezbollah a gabashin Lebanon, kusa da iyakar Syria.

1005 GMT — Turkiyya ta yi gargaɗi kan 'mummunan' yanayin da ake ciki a Falasɗinu

Halin da ake ciki a Gaza da aka yi wa ƙawanya da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye abu ne da ba a saba gani ba kuma "mai tsananin haɗari.

Tawagar Turkiyya a kotun duniya ICJ ta bayyana cewa, ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta da kuma kai kayan agaji ba tare da wani cikas ba.

Sabon wakilin Turkiyya na dindindin da aka nada a Majalisar Dinkin Duniya kana mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Ahmet Yildiz ya wakilci kasar inda ya gabatar da jawabin baka a taron ba da shawarwari kan shari'ar illoli da kuma manufofin Isra'ila a yankunan Falasdinawa da ta mamaye ciki har da Gabashin Kudus.

Yildiz ua yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a Gaza da kuma bude hanyoyin kai agaji ba tare da wata tangarda ba ga Falasdinawa, a yayin da watan Ramadan ke gabatowa.

"Abin takaici ne ganin rahotanni game da shirin gwamnatin Isra'ila na takaita addu'o'in musulmai a masallacin Haram al Sharif a cikin watan Ramadan," in ji shi a yayin taron jin ra'ayin jama'a a birnin Hague, inda ya kara da cewa "tsokanar" da wasu ministocin Isra'ila ke yi yana ''matukar haifar da damuwa. ."

Yayin da yake bayyana matsayin Ankara dangane da halin da Falasdinu ke ciki, Yildiz ya ce, Turkiyya ta ''damu matuka'' da manufofi da ayyukan Isra'ila na bai daya, wanda ya ''saba wa matsayin da ake ciki a Haram al Sharif (Masallacin Al Aqsa).''

0100 GMT — Sojin Isra'ila sun gabatar da shirin kwashe mutane yayin da Netanyahu ya sha alwashin mamaye Rafah

Sojojin Isra'ila sun gabatar da wani shiri na "kwashe" fararen hula daga Gaza, bayan da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce kai farmaki ta ƙasa kan birnin Rafah na kudancin Falasdinawa ya zama wajibi domin samun nasara baki ɗaya.

Gwamnatocin ƙasashen waje da ƙungiyoyin agaji sun sha bayyana fargabar cewa irin wannan farmakin zai janyo asarar rayukan fararen hula a Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.4 -- galibinsu da suka yi gudun hijira daga wasu yankuna -- suke samun mafaka a can.

Har ila yau, ita ce hanyar shigar da agajin da ake tsananin buƙata, inda ake shigar da kayayyakin daga maƙwabciyarta Masar.

Sojojin Isra'ila "sun gabatar wa da majalisar ministocin yaƙin wani shiri na kwashe jama'a daga yankunan da ake gwabzawa a Gaza, da kuma shirin gudanar da aikin ƙaddamar da hare-hare da ke tafe", a wata sanarwa da ta fito daga ofishin Netayahu a cikin harshen Hebrew a yau Litinin.

Sanarwar ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda za a kwashe fararen hular ko kuma inda za a kai su ba.

Sanarwar ta zo ne bayan da ƙwararru da Masar, Qatar da Amurka suka gana a birnin Doha, taron da ya kuma samu halartar wakilan Isra’ila da na Hamas, kamar yadda kafar yada labarai ta Masar mai alaƙa da gwamnatin Masar ta bayyana, wanda shi ne yunƙuri na baya-bayan nan da aka yi na ganin an cimma matsaya kafin watan Ramadan mai alfarma.

2311 GMT — Isra'ila ta sha alwashin kai hari kan ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon ko da kuwa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza

Ministan tsaron Isra'ila ya sha alwashin zafafa kai hare-hare kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Lebanon ko da an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza.

Kungiyar Hizbullah da ke musayar wuta da Isra'ila a tsawon yaƙin da take yi a Gaza, ta ce za ta dakatar da kai hare-hare kusan kullum a kan Isra'ila idan har aka tsagaita wuta a Gaza.

Amma Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce duk wanda ya yi tunanin tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza na nufin zai yi amfani a yankin arewacin ƙasar to "bai fahimci abin ba."

"Za mu ci gaba da ɓarin wutar da muke yi," in ji Gallant. Ya ce, akwai wata manufa mai sauƙi, ita ce ta kawar da Hizbullah daga kan iyakar Isra'ila, ko dai ta hanyar yarjejeniyar diflomasiyya ko kuma da ƙarfi.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda