1204 GMT — Masu zanga-zanga a Isra’ila na kira kan a hamɓarar da gwamnatin Netanyahu
‘Yan Isra’ila da suka gudanar da zanga-zanga a Yammacin Birnin Ƙudus a ranar Lahadi sun buƙaci a hamɓarar fa gwamnatin Benjamin Netanyahu da kuma gudanar da sabon zaɓe, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Masu zanga-zangar sun toshe ainahin ƙofar shiga birnin inda suke kira da a sake sabon zaɓe da kuma sauke firaiministan mai ci, kamar yadda Yedioth Ahronoth ta ruwaito.
“Muna son zaɓe” kuma “Muna son gwamnatin da ta san abin da take yi” na daga cikin abubuwan da masu zanga-zangar ke faɗi.
1043 GMT — An kashe sojojin Isra'ila biyu an raunata uku
Rundunar Sojin Isra’ila ta ce an ƙara kashe sojojinta biyu a yaƙin da ake yi a kudancin Gaza, kamar yadda ta bayyana a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce an kashe Sajan Nachman Meir Haim Vaknin mai shekara 20 da kuma Sajan Noam Bittan.
Wasu karin ƙananan sojoji biyu da babban soja ɗaya sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani abu a wani ramin ramin da ke yankin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.
1003 GMT — Mutane da dama sun rasu a hare-haren da Isra'ila ta kai sansanin gudun hijira na Nuseirat
Wani asibitin Gaza ya bayyana cewa, wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira da ke tsakiyar Falasdinu ya kashe akalla mutane 20.
Sanarwar da asibitin shahidai na Al Aqsa ya fitar ta ce "Mun samu asarar rayuka 20 tare da jikkata wasu da dama bayan wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wani gida na iyalan Hasan da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al Nuseirat da ke tsakiyar Gaza."
Shaidu sun ce an kai harin ne da misalin karfe 3:00 na safe agogon kasar.