Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2024
1449 GMT — Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya "yi gargadi da kakkausar murya kan duk wani yunƙuri na wargazawa ko rage" ayyuka da hurumin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta UNRWA bayan da Isra'ila ta zartar da dokar hana ayyukanta.
A cikin wata sanarwa da aka amince da ita, mambobi 15 sun nuna matukar damuwa kan dokar da majalisar dokokin Isra'ila ta amince da ita a ranar Litinin.
Majalisar ta bukaci gwamnatin Isra'ila da ta bi hakkinta na kasa da kasa, da mutunta gata da kariya na UNRWA tare da yin aiki da alhakin da ya rataya a wuyanta na ba da izini da sauƙaƙe cikakken, cikin sauri, aminci da rashin cikas ga taimakon jinƙai a duk ayyukanta a ciki da kuma duk faɗin Gaza. Tafi."
0800 GMT — 'Yan Syria da ke tserewa daga Lebanon suna iya fuskantar tsangwama idan suka koma ƙasarsu — HRW
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta yi gargaɗin cewa 'yan Syria da ke tserewa daga hare-haren da Isra'ila take kai wa ƙasar Lebanon suna iya fuskantar bala'i a ƙasarsu a yayin da fiye da 'yan Syria 355,000 suka koma gida a cikin wata ɗaya.
"'Yan Syria da ke tserewa daga Lebanon, musamman maza, suna fuskantar hatsarin ɗauri da cin zarafi daga hukumomin Syria," a cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
"Mutuwar da mutanen da aka ɗaure suke yi a gidajen yari sakamakon yanayin da ke cike da zargi ta nuna babban hatsarin da ke cikin komawa gida da kuma fuskantar tsarewa da cin zarafi da tsana ga mutanen da suka koma," a cewar mataimakin daraktan HRW a Gabas ta Tsakiya, Adam Coogle.
0045 GMT — Gwamnatin Falasɗinu na shirin gurfanar da Isra'ila a gaban Kwamitin Tsaro na MDD kan haramta ayyukan hukumar UNRWA
Fadar shugaban ƙasar Falasɗinu ta ce tana shirin ɗaukar mataka diflomasiyya domin yin martani kan matakin majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset na haramta aikin hukumar da ke kula da Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA ya ruwaito cewa fadar shugaban ƙasar ta yanke shawarar gaggauta tuntuɓar ƙasashen da suka bai wa hukumar kula da Falasɗinawa matsuguni domin yiwuwar gabatar da batun a gaban Kwamitin Tsaro da kuma Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.
The decision on UNRWA's presence is linked to resolving the Palestinian issue in accordance with international legitimacy, according to the presidency.
Fadar shugaban ƙasar na Falasɗinawa ta ce za ta ɗora alhakin duk wani abu mara daɗi da ya faru bayan haramta hukumar a kan gwamnatin Isra'ila.
Ta ƙara da cewa "dukkan hare-haren da Isra'ila take ci gaba kai kai wa ba za su tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalinta ba, sai dai su ƙara mata zaman ɗarɗar da zulumi a yankin" muddun ba a yi wa Falasɗinawa adalci ba."
Ƙarin labarai👇
0152 GMT — Jakadan Turkiyya a MDD ya gabatar da buƙatar daina sayar wa Isra'ila makamai
Wakilin Turkiyya na dindindin a MDD ya ce Turkiyya tare da gamayyar wasu manyan ƙasashe, sun fitar da wata takardar haɗin-gwiwa inda suka yi kira a daina sayar wa Isra'ila makamai.
Da yake gabatar da jawabi a wurin muhawara game da "Halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, ciki har da matsayin Falasɗinawa," Ahmet Yildiz ya jaddada cewa Isra'ila ta jefa yankin cikin bala'in yaƙi kuma ta aikata manyan laifukan yaƙi.
"Mun yi wannan kira na haɗin-gwiwa ne domin a ɗauki matakai nan-take na daina sayar da makamai ga Isra'ila ta kowace fuska saboda tana amfani da su a yankin Falasɗinawa da ta mamaye, ciki har da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, lamarin da ya saɓa wa doka mai lamba ES-10/24 ta ranar 18 ga Satumban 2024 ta Babban Zauren MDD," in ji shi.
"Wannan zai taimaka wajen kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi da kuma keta haƙƙoƙin Falasɗinawa fararen-hula a Gaza da sauran yankin Falasɗinawa da ta mamaye da Lebanon, kana ya daƙile tayar da jijiyoyin wuya a yankin."