Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa 54, adadin wadanda suka mutu a Gaza ya haura 38,800 / Hoto: AA / Photo: Reuters

1434 GMT — Netanyahu na Isra'ila ya hana samar da asibiti don duba yaran Gaza da aka jikkata

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ƙi amincewa da kafa wani asibiti na wucin-gadi don duba yaran Falasdinawa da suka jikkata a ci gaba da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

"Netanyahu ya sanar a rubuce cewa bai amince da kafa asibiti ga al'ummar Gaza a cikin Isra'ila ba - don haka ba za a kafa shi ba," in ji ofishinsa a cikin wata sanarwa.

Ofishin Ministan Tsaron Ƙasar Yoav Gallant ya sanar da kafa asibitin wucin-gadin ne, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda rufe hanyar Rafah ta Gaza zuwa Masar na tsawon lokaci.

1048 GMT — Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa 54, adadin wadanda suka mutu a Gaza ya haura 38,800

Akalla karin Falasdinawa 54 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya sa adadin wadanda suka mutu ya kai 38,848 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi ruwan bama-bamai.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu mutum 89,459 ne suka jikkata

"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 54 tare da raunata wasu 95 a cikin 'kisan gilla' uku da aka yi wa iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata," in ji ma'aikatar.

0730 GMT — Ministan Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi ya kutsa Masallacin Ƙudus yana barazanar dakatar da tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza

Ministan Tsaron Ƙasa na Isra'ila mai tsatsauran ra'ayi ya kai farmaki a harabar Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus, inda ya yi barazanar kawo cikas ga tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza.

Itamar Ben-Gvir, shugaban masu tsattsauran ra'ayi, ya ce ya je yankin ne domin yin addu'ar dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su "amma ba tare da wata yarjejeniya ba, ba tare da sun miƙa wuya ba."

Matakin dai na barazanar kawo cikas ga tattaunawar da ke da muhimmanci da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Masu shiga tsakani na Isra'ila sun sauka a birnin Alkahira ranar Laraba domin ci gaba da tattaunawar.

Ziyarar ta kuma zo ne kwanaki kadan kafin Firaminista Benjamin Netanyahu ya tashi zuwa Amurka, inda zai yi jawabi ga majalisar dokokin kasar.

Ben-Gvir ya ce yayin da yake tsaye a gaban hasumayar Dome of the Rock "yana addu'a da aiki tukuru" don tabbatar da cewa Netanyahu ba zai miƙa wuya ga matsin lambar da ƙasashen duniya ke masa ba, kuma zai ci gaba da kai farmakin soji a Gaza.

Palestinians mourn after Israeli fighter jets hit United Nations Relief and Works Agency for Palestine Refugees in the Near East (UNRWA) school

0700 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe babban jagoran ƙungiyar Jamaa Islamiya na Lebanon

Kafofin yada labaran Labanon sun bayyana cewa, an kashe wani babban jigo na kungiyar Jamaa Islamiya ta kasar, a wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a gabashin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran Labanon na NNA ya rawaito cewa Mahmud Mohammad Jbara, babban jagoran kungiyar, an kashe shi ne a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan motarsa ​​a yankin yammacin Bekaa da ke gabashin kasar Lebanon.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ta'azzara a yankunan kan iyakar Lebanon da Isra'ila sakamakon barazanar da babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya yi a ranar Larabar da ta gabata na kai hare-hare kan sabbin matsugunan Isra'ila idan sojojinta suka ci gaba da kai hari kan fararen hula a Lebanon.

0800 GMT — Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce "dole a daina zubar da jinin da ake yi a Gaza a yanzu", tana mai ƙarawa da cewa dubban Falasɗinawa fararen-hula sun rasa rayukansu sakamakon yaƙin da Isra'ila take yi a yankin.

"Al'ummomin Gaza ba za su iya ci gaba da jure wa wannan yaƙi ba, kuma 'yan'adam ba za su iya ci gaba da zuba idanu suna kallo ba," in ji jami'ar ta EU a jawabin da ta yi wa Majalisar Dokokin Turai a birnin Strasbourg na Faransa.

"Muna buƙatar a yi gaggawar daina yaƙi. Muna buƙatar a saki Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su, sannan mu ɗauki mataki na gaba."

2101 GMT — Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar da hankali" a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Amurka ta sanar da wasu sabbin takunkumin hana biza ga Isra'ilawan da suka tayar da "tarzoma" a kan Falasdinawa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, tana mai kira ga Isra'ila da ta dauki mataki kan wadannan mutane.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller ya shaida wa manema labarai cewa "Wannan lamari ne game da ƙaruwar tashe-tashen hankula da muka gani cikin bakin ciki a cikin 'yan watannin da suka gabata da kuma bukatar Isra'ila ta ƙara himma wajen daukar mataki a kan mutanen da suke aikata hakan."

Matakan sun hana wasu 'yan Isra'ila da 'yan'uwansu shiga Amurka. Miller ya ce gwamnatin Isra'ila ta dauki wasu matakai na murkushe tashe-tashen hankula a Yammacin Gabar Kogin Jordan, kamar kama wasu masu aikata laifuka.

"Amma wadannan matakan ba su isa ba," in ji shi.

Daga cikin wadanda wannan sabon takunkumin ya shafa har da tsohon sojan Isra'ila Elor Azaria, wanda aka yanke masa hukuncin daurin watanni tara a gidan yari saboda harbi da kashe wani Bafalasdine da ya ji rauni a shekarar 2016.

Akalla Falasdinawa 81 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan, in ji jami’an kiwon lafiya. / Hoto: AA

2230 GMT — Rasha ta ce Iran da Lebanon da Hizbullah ba sa son yaƙi da Isra'ila

Babban jami'in diflomasiyyar Rasha ya ce kungiyar Hizbullah ta Lebanon da Iran da gwamnatin Lebanon ba sa son "yaƙi mai cike da rudani - kuma akwai shakkun cewa wasu mutane a Isra'ila na kokarin cimma hakan."

Sergey Lavrov ya shaida wa taron manema labarai na Majalisar Dinkin Duniya cewa, Rasha na yin duk mai yiwuwa don kwantar da hankula.

Lavrov ya ce gwamnatin da ta gabata ta Iran da kuma sabon shugaban kasar "suna nuna wani matsayi da ke nuna cewa Iran ba ta da sha'awar ci gaba."

Ba tare da ba da suna ba, Lavrov ya ce manazarta a Amurka da Turai sun ce "ruruwar rikicin kamar yadda abubuwan da ke faruwa a zahiri suka nuna, wani abu ne da Isra'ila ke sha'awarsa."

Lavrov ya kara da cewa, "Hizbullah ta kasance mai kamun kai matuka a cikin ayyukanta, kuma shugabanta Hassan Nasrallah ya ba da jawabai da dama wadanda suka tabbatar da wannan matsayi."

“Duk da haka, yana jin cewa ana yunkurin ta da musu hankali da kuma tunzura su cikin wani cikakken salon tsokana,” in ji shi.

TRT Afrika da abokan hulda