Isra’ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: AA / Photo: Reuters

Talata, 13 ga watana Agusta, 2024

Kwararru kan harkokin kiwon lafiya na Isra'ila sun yi rajistar ƙaruwar shan miyagun ƙwayoyi da barasa da kuma wasu ɗabi'u na jaraba a tsakanin sojojin Isra'ila, suna masu alaƙanta ƙaruwar hakan da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza na Falasdinu.

Isra'ilawan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya zanta da su, sun ce suna amfani da ƙwayoyin ne a matsayin wani yunƙuri na guje wa gaskiyar abin da ke faruwa da mantawa da yaƙi da kuma kawar da fargabar da suke ciki.

Masanin ilimin lafiyar ƙwaƙwlwa Shaul Lev-Ran, wanda ya kafa Cibiyar Magance Jarabar Shan Ƙwaya ta Isra'ila (ICA), ya ce "a matsayin martani na dabi'a kan damuwa da kuma neman taimako, mun ga wani gagarumin tashin hankali a cikin amfani da wasu abubuwan kwantar da hankali da ke zama jaraba. ”

Wani bincike da tawagarsa ta gudanar ya gano "dangantaka tsakanin fallasa kai tsaye ga abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba da kuma karuwar amfani da abubuwan maye" kusan kashi 25 cikin 100.

Lev-Ran ya ce ICA ta gano hauhawar amfani da "magani ba bisa ƙai’da ba da mugayen ƙwayoyi d, barasa, ko halayen jaraba kamar caca."

A cikin 2022, ɗaya cikin bakwai na Isra'ilawa suna fama da jarabar shaye-shayen ƙwayoyi. Duk da haka, daya daga cikin Isra'ilawa hudu, tun daga lokacin, sun kara yawan amfani da kayan maye, bisa ga binciken, wanda aka gudanar a watan Nuwamba da Disamba na bara a kan samfurin wakilcin mutum 1,000 na Isra'ila.

A cewar Lev-Rab, Isra’ila ta riga ta kasance “a farkon annobar da yawancin jama’a za su soma shaye-shayen abubuwa.”

Binciken ya gano cewa amfani da magungunan barci da magungunan kashe radadi su ma sun yi tashin gwauron zabo - da kashi 180 da kashi 70 cikin 100, bi da bi.

Majalisar Dinkin Duniya ta gaza wurin kafa ƙasar Falasɗinu — Abbas

Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya caccaki Majalisar Dinkin Duniya dangane da gazawarta wurin kafa ƙasar Falasɗinu tare da ɗora alhakin hakan kan matsin lambar da Amurka ke yi.

“Amurka ta gaza a aikinta na bayar da mafita ɗaya ko kuma samar da matsaya wadda za ta tabbatar da samar da ‘yancin Falasɗinawa da kuma kafa ƙasar,” kamar yadda Abbas ya bayyana a lokacin da suka yi wata tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow.

Duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu yara ne da mata.

0720 GMT –– Ɗaruruwan Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna ciki har da ministoci biyu sun kutsa cikin harbar Masallacin Birnin Ƙudus da ke Gabashin Ƙudu, tare da rakiyar dakarun Isra'ilam domin gudanar da ibada. Lamarin ya harzuƙa Falasɗinawa Musulmai da ke harabar Masallacin.

Jaridar Ynet da ake wallafawa a shafin intanet ta ce Ministan Tsaron Ƙasar mai ra'ayin riƙau Itamar Ben-Gvir, da Ministan jam'iyyar Otzma Yehudit Yitzhak Wasserlauf da kuma mamba a majalisar dokokin Knesset a jam'iyyar Likud Amit Halevi sun bi sahun 'yan kama-wuri-zauna kimanin 800 wajen shiga harabar masallacin inda suka yi addu'o'i na ibadar Talmud.

'Yan kama-wuri-zauna sun shiga Masallacin Ƙudus ne domin yin biyayya ga kiraye-kirayen da Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi suka a gare su don su gudanar da addu'o'i na bikin Tisha B'Av, wanda Yahudawa suke yi duk shekara don tunawa da bala'o'i daban-daban da suka faru a tarihin Yahudawa, in ji Wafa.

Sun shiga masallacin ne ta ƙofar yamma da ake kira Ƙofar Al-Mugharbah, wadda yawancin lokuta ake amfani da ita wurin shiga harabar masallacin, a cewar Wafa.

2207 GMT — Isra'ila ta bai wa 84% na Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu — MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girman mamayar da sojojin Isra'ila suke yi wa yankin Gaza, tana mai cewa an kori kusan kashi 84 daga yankin.

Da yake bayani kan alƙaluman da Ofishin Babban Mai Kula da Harkokin Jinƙai na Majalisar (OCHA) ya tattara, mataimakin kakakin ofishin Farhan Haq ya shaida wa manema labarai cewa "luguden wuta da kuma kutsen da Isra'ila take yi a Gaza na ci gaba da kashewa da jikkatawa tare da korar Falasɗinawa daga matsugunansu – da kuma rusa gidajensu da sauran gine-gine da suka dogara a kansu."

Ya ce, "Sau biyu sojoji suna bayar da umarni ga mutane su fita daga Khan Younis a ƙarshen mako, zuwa yankunan da a baya galibi aka umarci mutane su fice daga cikinsu."

Wannan lamari ya shafi yankuna 23 da wurare 14 da ke samar da ruwa da tsaftar jama'a da kuma makarantu huɗu.

"Jimilla, sojojin Isra'ila sun kori mutane daga wurin da ya kai girman murabba'in kilomita 305, wato kusan kashi 84 na yankin Zirin Gaza," in ji shi.

Ana kai gawawwaki da mutanen da suka jikkata Asibitin Shahidai na al-Aqsa da ke Deir al-Balah, ciki har da jarirai da Isra'ila ta harba wa bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij / Hoto: AA

2335 GMT — Wata 'yar siyasa a Finland ta soki gwamnati kan ƙin ɗaukar mataki a yaƙin Gaza

Nasima Razmyar, mataimakiyar shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta Finland kuma 'yar majalisar dokoki, ta caccaki gwamnatin ƙasar kan gaza sukar Isra'ila bisa kisan kiyashin da take yi a Gaza, inda ta zargi mahukunta a Helsinki da zama 'yan amshin-shata, kamar yadda kafofin watsa lamarai suka ruwaito.

Razmyar ta bayyana matuƙar ɓacin ranta kan kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa da kuma rashin kataɓus na ƙasashen duniya.

"Rashin imanin da ake yi a yaƙin Gaza abu ne da ba zai misaltu ba. Mun zama kamar kurame, Al'umma na ɗanɗana kuɗarsu, suna fama da bala'in yunwa sannan gidajensu sun zama toka— wannan lamari ne da ke da wahalar fahimta domin kuwa ko da yaushe a cikin yaƙi suke," kamar yadda jaridar Helsinki Times ta ambati ta tana cewa.

'Yar siyasar ta ce duk da kiran da Kotun Ƙasa da Ƙasa ta (ICJ) ta yi kan a tsagaita wuta da kuma bayyana mamayar da ake yi wa yankunan Falasɗinawa a matsayin haramtacciya, Isra'ila tana ci gaba da kashe su.

TRT Afrika da abokan hulda