'Yan kasar Turkiyya da iyalansu wadanda aka kwaso daga Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankin sun isa Istanbul daga Masar.
Jirgin saman Turkish Airlines dauke da 'yan kasar Turkiyys 142 wadanda suka tsallaka Masar ta Mashigar Rafah sun sauka a filin jirgin saman Istanbul Dda sanyin safiyar Litinin bayan ya taso daga filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Alkahira.
Jami'an Ma'aikatar Harkokin Waje Turkiyya da na Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala'i (AFDA) ne suka tarbe su.
Wasu daga cikinsu sun yi ta hawaye a yayin da suka sauka daga jirgi.
Ranar 19 ga watan Nuwamba, Turkiyya ta kwaso 'yan kasarta 42 daga Gaza.
Isra'ila ta ci gaba da kai are-hare Gaza ranar Juma'ar da ta gabata bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hamas ta Falasdinawa.
Hare-haren da ta kaddamar ranar 7 ga watan Oktoba sun kashe Falasdinawa akalla 15,500, galibinsu kananan yara da mata bayan harin ba-zata da Hamas ta kai mata.










