Umarnin ficewa daga Isra'ila ya tilasta wa Falasɗinawa ficewa daga tsakiyar Gaza / Photo: Reuters

1519 GMT — Umarnin ficewa daga Isra'ila ya tilasta wa Falasɗinawa ficewa daga tsakiyar Gaza

Dubban Falasdinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza sakamakon sabbin umarnin ficewa da Isra'ila ta yi, lamarin da ke ƙara ta'azzara halin jinƙai a wani yanki da tuni ya cika da 'yan gudun hijirar da ke tsere wa farmaki a kudancin kasar.

Sojojin Isra'ila, waɗanda a yanzu suka ƙwace kusan ɗaukacin yankunan a cikin kusan watanni 10 na yaƙin, sun shafe makonni da dama suna ƙaddamar da manyan hare-hare a yankunan da a baya suka yi ikirarin "kore mayaƙan Hamas."

A harin na baya-bayan nan da ta kai, Isra’ila ta umarci mazauna garin a ranar Lahadi da su ƙaurace wa Al-Bureij da ke arewa maso gabashin Deir.

"Me ya saura? Deir? Deir cike take da mutane, kowa yana Deir, duk Gaza. Ina mutane za su tafi?" Aya Mansour ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a Deir bayan ta gudu daga Bureij.

0935 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin Isra'ila a Gaza ya kai 39,363

Aƙalla Falasɗinawa 39,363 aka kashe a kusan tsawon wata 10 da a Isra'ila ta shafe tana yaƙi a Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu da ke yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa.

Adadin waɗanda suka mutu ya haɗa da mutuwar mutum 39 a cikin sa'o'i 24, a cewar alkaluman ma'aikatar, wanda ya kuma bayyana mutum 90,923 da suka samu raunuka a Gaza tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

0416 GMT –– Tsoron harin Isra'ila ya tilasta soke tashin jirage a Beirut na Labanon

An soke ko jinkirta tashin jiragen sama a birnin Beirut inda kamfanin jiragen sama na gabas ta tsakiya (MEA) na kasar Labanon ya ce kawo cikas ga jadawalinsa na da alaƙa da hadarin inshora, yayin da ake takun saka tsakanin Isra'ila da Hizbullah.

Lufthansa ya ce ya dakatar da bulaguro a hanyoyi biyar na zuwa ko fita daga Beirut ta kamfanonin jiragen sama na Swiss International Air Lines, Eurowings da Lufthansa har zuwa ranar 30 ga Yuli "cikin taka tsantsan".

Hukumar kula da bayanan jirgin da ke birnin Beirut da shafin intanet na sa ido kan jirgin Flightradar24 sun nuna cewa kamfanin jirgin saman Turkiyya ya kuma soke tashin jirage biyu a daren ranar Lahadi.

0007 GMT –– Netanyahu yana jawo tsaiko wajen kwashe yara marasa lafiya 150 daga Gaza zuwa UAE

Kamfanin dillancin labaran Isra''ila ya rawaito cewa firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya jinkirta kwashe kananan yara Falasdinawa 150 marasa lafiya da waɗanda suka jikkata daga Gaza zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin yi musu magani.

A ranar Litinin ne ya kamata yara marasa lafiya daga Gaza su tashi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa daga Isra'ila, amma bayan abin da ya faru a Majdal Shams, Firaiminista Netanyahu ya ba da umarnin a jinkirta tafiyarsu," in ji hukumar yada labaran kasar.

Ta ce Netanyahu ya yanke shawarar ɗage tashin yaran ta filin jirgin saman Ramon na Isra'ila. Hukumar ta ba da sabuwar ranar tashi ga yara marasa lafiya. Kawo yanzu dai babu wani bayani daga UAE kan lamarin.

TRT Afrika da abokan hulda