| Hausa
DUNIYA
3 MINTI KARATU
Wani Kirista a Sweden ya ki sayar wa mutumin da ya kona Kur'ani lemon kwalba
Wani Kirista dan ciranin Iraki a babban birnin Sweden ya ki ya sayar wa Salwan Momika, mutumin da ya kona Alkur'ani, lemon kwalba daga shagonsa, saboda jin takaicin abin da ya yi na wulakanta Musulunci.
Wani Kirista a Sweden ya ki sayar wa mutumin da ya kona Kur'ani lemon kwalba
Momika, dan asalin kasar Iraki da ke zaune a Sweden ya kona Kur'ani karkashin kariya da 'yan sanda suka ba shi a gaban Babban Masallacin Stockholm ranar Sallar Layya. / Photo: Reuters Archive / Reuters Archive
25 Yuli 2023

Wani Kirista dan kasar Iraki ya ki sayar wa mutumin da ya kona Kur'ani a Sweden lemon kwalba daga shagonsa, saboda jin takaicin abin da ya yi na wulakanta Musulunci.

Ibrahim Sirimci, wanda ke da kantin sayar da abinci a babban birnin Sweden Stockholm, ya yi kememe ya ki sayar wa Salman Momika lemon kwalbar.

Mai kantin sayar da abincin ya nadi bidiyon abin da ya farun tare da yadawa a shafukan sada zumunta.

Kazalika wani Kiristan dan kasar Iraki da shi ma yake cikin kantin a lokacin, ya shaida wa Momika cewa "Ni ma dan Iraki ne, ni Kirista ne. Abin da ka yi abin kunya ne da tur. Ka ci mutuncin Musulunci. Ka bata mana rai kamar yadda ka bata wa mutane da dama."

Yayin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Sirimci ya ce Momika ya je kantinsa ne sayen lemon kwalba kuma da ya gane shi sai ya ce ba zai sayar masa ba.

Ana neman siyasantar da kona Kur’ani da ake yawan yi a Turai

Sirimci ya ce: "Ya zo kantina don ya sayi lemon kwalba. Na gane shi sai na ce masa, 'Kai ne wanda ka kona Kur'ani, don haka ba zan sayar maka da lemo ba."'

Momika, dan asalin kasar Iraki da ke zaune a Sweden ya kona Kur'ani karkashin kariya da 'yan sanda suka ba shi a gaban Babban Masallacin Stockholm ranar Sallar Layya.

A ranar 20 ga watan Yuli ne Momika ya sake yaga Kur'ani tare da tutar kasar Iraki a yayin da 'yan sanda suke ba shi kariya a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke birnin Stockholm.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran