| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Shugaban Turkiyya da na Mauritaniya sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashensu da batutuwan yanki
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Mauritaniya Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashen da batutuwan yanki, kamar yadda ofishin sadarwa na Turkiyya ya bayyana ranar Laraba.
Shugaban Turkiyya da na Mauritaniya sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashensu da batutuwan yanki
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Mauritaniya Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani sun tattauna ta waya ranar 24 ga Yuni, 2026. / User Upload

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Mauritaniya Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashensu da batutuwa da suka shafi yanki, kamar yadda Ofishin Sanadrwar Turkiyya ya bayyana ranar Laraba.

A wata tattaunawa ta waya, Erdogan ya ce Turkiyya da Mauritaniya za su iya ƙarfafa dangatakarsu ta hanyar ɗaukar matakai ƙwarara a wasu fannoni, musamman ta cinikayya da noma da harkar kamun kifi da tsaro da masana’antar kare ƙasa , kamar yadda ofishin ya bayyana a shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal.

Shugaba Erdogan ya ƙara da cewa ƙasashen biyu za su ci gaba da aiki tare nan gaba domin ƙarfafa haɗin-kai a al’amuran ƙasa da kasa.