A ’yan shekarun nan, siyasar Nijeriya na ɗaukar sabbin salo tun daga sauye-sauye a tsarin jam’iyyu, sauya sheƙa, har zuwa yadda biyayya ga manyan ’yan siyasa ke raguwa, yayin da matasa da sababbin masu neman takara ke ƙara fitowa fili.
A gefe guda kuma, kafofin sada zumunta sun zama muhimman kayan aiki wajen yaɗa ra’ayoyi da farfaganda, waɗanda ke yin tasiri ga zaɓin jama’a. Haka kuma, waƙoƙin siyasa sun ci gaba da taka rawa wajen jan ra’ayi da sukar abokan hamayya.
Sai dai a ƙasa kamar Nijeriya mai jihohi 36 da babban birninta Abuja, babbar tambaya ita ce: me ya sa aka fi jin amon siyasar jiha ɗaya tak, wadda ta mamaye kusan dukkanin dandalolin tattaunawa?
Masu sharhi da dama sun ce, kamar yadda ake cewa “Kano Tumbin Giwa, ko da me ka zo an fi ka,” haka ma siyasar jihar take da salo na musamman. A taƙaice: Siyasar Kano, sai Kano.
Malam Kabir Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Jihar Kano ya bayyana cewa tun daga Jamhuriya ta Farko da ta Biyu, siyasar Kano ta kasance ta daban.
Ya ce yawan rigingimu da saɓani tsakanin jam’iyyu ne ya sa hankalin ’yan ƙasa ke karkata zuwa gare ta, har ma wasu jihohi ke kallonta a matsayin madubi.
Ya ƙara da cewa Jihar Kano na da matuƙar muhimmanci a siyasar Nijeriya saboda yawan jama’arta da kuma tasirinta a Arewacin ƙasar. Duk wani sauyi da ya faru a Kano na iya shafar siyasar ƙasa baki ɗaya.
Wannan ne ya sa, ko a matakin gwamnatin tarayya, burin duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa shi ne samun rinjayen ƙuri’un Kano domin ya yi wa abokan hamayya fintinkau.
Sai dai duk da haka, masu sharhi da dama sun yarda cewa a wannan karo an fuskanci wani sabon saɓani da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin jihar — wato rabuwar kai tsakanin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, waɗanda aka daɗe ana kallonsu a matsayin uba da ɗa a siyasa ko ma fiye da siyasa, bayan shafe kusan shekara 40 suna tare.
Wannan lamari ya haifar da muhawara: wasu na ganin kamar Gwamna Abba ya ci amanar Kwankwaso, yayin da wasu ke cewa wannan al’amari abu ne na yau da kullum a siyasa.
A cikin wannan makon ma, al’amura sun sake ɗaukar sabon salo bayan sauye-sauyen siyasa da suka faru. Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, ya koma jam’iyyar ADC kwanaki biyu kacal bayan komawar Kwankwaso cikinta. Har ma an ga Kwankwaso ya raka shi zuwa mazaɓarsa domin yin rijista.
Ga wanda ya ga cakwakiyar da aka yi a 2023 wacce kamar shekaranjiya take, inda Kwankwaso da Abba suke tif da taya, yayin da Gawuna yake sansanin Ganduje, tsohon gwamnan da ba sa ga maciji da Kwankwaso, a yau kuma ya ga Abba tare da jam’iyyar su Ganduje, shi kuma Gawuna ya koma wajen Kwankwaso, zai san cewa lallai ba abin da mai rai ba zai gani ba, kuma idan akwai sauran rai da lafiya da abin da lafiya za ta ci, to a iya cewa kallo yana gaba.
A bangaren sauran jihohi ma, ba wai siyasarsu ba ta da tasiri ba ne, sai dai a iya cewa mafi yawa tasu siyasar ta yaƙin sunƙuru ce.
A lal misali a jihar Bauchi, wani hayaƙin gumurzun da za a yi tsakanin manyan ‘yan takara tuni ya fara turnuƙe sararin samaniyar jihar, kamar yadda makamancinsa ke tashi a wasu jihohin ma daban.
Masu fashin baƙi na cewa duk da wannan sabon salo a fagen siyasar Nijeriya, akwai kalubale kamar:
Yiwuwar samun ƙarin rikice-rikice a cikin wasu jam’iyyu, da tasirin da kuɗi ka iya yi a siyasa da ma samun saɓani a tsakanin wasu bangarori.
Amma a lokaci guda, wannan sauyi na kawo dama ga bunƙasar dimokuradiyya, musamman idan matasa suka ci gaba da shiga da ba da himma ana damawa da su.
A takaice, siyasar Nijeriya, musamman a Kano, na shiga wani sabon zamani. Wannan sauyi na iya zama mai anfani idan aka yi amfani da shi da kyau.
Tambayar ita ce: Shin wannan sabon salon yana da tasiri wajen samar da shugabanci na gari da cin amfanin dimokuradiyya, ko kuwa dai batu ne kawai na gwada ƙwanji da ƙoƙarin dafe madafun iko don biyan bukatar wasu ‘yan tsiraru?












