Hukumar zaɓen Nijeria Mai Zaman Kanta INEC ta sanar da Gwmanan Jihar Ekiti Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara karo na biyu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon ya nuna cewa gwamnan ya samu nasarar ne da kuri’u 319,224, inda ya doke sauran abokar takararsa.
Dan takarar jam’iyyar PDP Mr Wole Oluyede shi ne ya zo na biyu da kuri’u a 40,543, kamar yadda Babbar Jami’ar Zaben Farfesa Adenike Oladiji ta bayyana a cikin daren Lahadin nan a Ado Ekiti, babban birnin jihar ta Ekiti.
Jami’iyyar ADC ce ta zo ta uku a zaben na gwmanan Jihar Ekiti, inda dan takararta Ambassador Dare Bejide ya samu kuri’u 12,872, a cewar INEC.
Farfesa Adenike ta bayyana cewa, jumullar masu kada kuri’a 384940 aka tantance a zaɓen na ranar Asabar, yayin da kuri’un da aka kaɗa daidai suka kasance 375,777, sannan aka ƙi amincewa da kuri’u 6,332 da suka lalace.
Fiye da masu kaɗa ƙuri’a miliyan ɗaya ne suka cancanci jefa ƙuri’a a zaɓen, wanda ake gudanarwa a rumfunan zaɓe 2,445 da ke faɗin jihar.
Me ya sa zaɓen Ekiti ya sha bambam da na sauran jihohi?
A shekarar 2010, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen Gwamna Segun Oni bayan ya shafe fiye da watanni 41 yana mulki.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Dakta Kayode Fayemi ne ya lashe zaɓen, kuma ta ba da umarnin a miƙa masa mulki nan take.
Sai dai, INEC ta shirya sake gudanar da zaɓe a wasu wuraren da aka samu takaddama, wanda daga ƙarshe ya sa Fayemi ya zama gwamnan jihar a shekarar 2010.
Wannan ya sa jadawalin zaɓe a Jihar Ekiti ya sauya.














