| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Peter Obi ya bayyana shirin ficewa daga jam'iyyar ADC
Ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, yana mai ambato ƙazancewar yanayin siyasa a ƙasa da rikicin da aka kunna musu a cikin jam'iyyar ADC. Sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba.
Peter Obi ya bayyana shirin ficewa daga jam'iyyar ADC
Peter Obi ya sanar da aniyar ficewa daga ADC, sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba. / Reuters / Reuters

Ɗaya daga ‘yan siyasar da ke kan gaba wajen neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a zaɓukan 2027 Peter Obi ya sanar da shirinsa na fita daga jam'iyyar hamayya ta ADC.

Ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, yana mai ambato ƙazancewar yanayin siyasa da rikicin da aka kunna musu a cikin jam'iyyar ta ADC. Sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba.

Peter Obi, wanda ya yi takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023 a jam'iyyar LP, ya fita daga jam'iyyar sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ya addabi jam'iyyar.

Ya ce zai fita ne ba don shugaban ADC David Mark ko Atiku Abubakar sun yi masa wani abu ba, sanna ya ce zai ci gaba da mutunta su.

Da tsakar daren Lahadi ne shi ma wani jigo a ADC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayanna shirin ficewa daga ADC, da sanar da tattaunawa da jam'iyyun NDC da PRP da yiwuwar komawa cikinsu.

A baya bayan nan ana yawan yada raɗe-raɗin cewa Obi da Kwankwaso za su fice daga ADC su koma wata jam'iyyar don yin takarar shugaban ƙasa da mataimaki.

Sai dai a cikin sanarwar, tsohon gwamnan na Jihar Anambara ya bayyana cewa bai damu sai ya zama shugaban kasa ko mataimaki ko shugaban majalisar dattijai ba.

“Na dai damu ne sosai wajen ganin al’ummar da za ta rarrashi uwar da aka yi garkuwa da ‘ya’yanta ko aka kashe su a kan hanyarsu ta zuwa makaranta ko aiki. Na damu na ga Nijeriyar da jama’a ke rayuwa ba a sansanonin mutanen da suka rasa mahallansu ba, sai dai rayuwa a gidajensu,” a cewar Obi.

“Sai dai duk da wadannan matsaloli, ina da cikakken kuduri, kuma na amince cewa Nijeriya za ta zama kasa mai shugabanci na gari bisa adalci, da tausayi da damammki bisa daidaito,” in ji shi.