Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a yi garambawul ga tsarin shugabanci na duniya, yana mai kira da a samar da wakilci ga Afirka a kujerun dindindin na Kwamitinr Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gyara cibiyoyin kuɗi a bangarori da dama.
"Dole ne mu gyara tsarin harkokin kuɗi na duniya wanda masu kuɗi suka ƙirƙira, kuma dole ne mu samu wakilci da zai dinga duba buƙatun ƙasashe masu tasowa, musamman a Afirka," in ji Guterres ga mahalarta taron Unstoppable Africa 2026, wanda aka gudanar a gefen Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, UNGA karo na 81 a New York.
Guterres ya jaddada cewa, nahiyar ta kasance "wadda ta yi fama da mulkin mallaka har sau biyu," yana mai bayyana cewa take ‘yancinta a baya ya sanya ƙasashen Afirka rashin samun kujera a teburin majalisar lokacin da aka kafa cibiyoyin ƙasa da ƙasa bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Kazalika ya ce Kwamitin Tsaro na MDD da cibiyoyin kuɗi na duniya sun gaza nuna alƙaluma da sha'awar Afirka, yana mai tabbatar da cewa dole ne a bai wa nahiyar kujeru na dindindin don taka rawa kai-tsaye wajen yanke shawara a duniya.
Ma'adanai masu mahimmanci, sauyin da ake sabuntawa
Da yake magana kan sauyin tattalin arziki, Guterres ya bayyana cewa kasuwannin duniya suna samun gaggarumin sauyi daga yin kasuwanci a Afirka kawai zuwa "yin kasuwanci da Afirka."
Duk da tsaikon da duniya ta samu sakamakon yaƙe-yaƙe a Ukraine da Gabas ta Tsakiya, Guterres ya ce tattalin arzikin Afirka ya haɓaka da kashi 4.4 cikin 100 a bara, inda aka kiyasta kusan samun dala biliyan 230 a wannan shekarar a kasuwancin da aka yi ƙarƙashin Yankin Cinikayya Marar Shinge ta Afirka, wanda hakan ya samar da dama ta riƙe darajar tattalin arziki a cikin gida maimakon dogaro da fitar da albarkatun ƙasa.
A bangaren albarkatun ƙasa, Guterres ya yi gargaɗi game da ci gaba da ci da gumin kasashen Afirka da ake yi a yayin da ake ƙara samun gasa a fannin siyasa.
"Dole ne mu tabbatar da cewa albarkatun ƙasa na Afirka, musamman ma'adanai masu mahimmanci, suna da daraja a cikin gida da kuma samar da ayyukan yi, maimakon kawai a dinga jigilar su zuwa ƙasashen waje."
Ya yi nuni kan gagarumin ci gaban da aka samu a fannin makamashi da ake sabuntawa da kuma fasahar zamani a faɗin nahiyar, inda ya ambato ƙasar Kenya wadda ke samar da fiye da kashi 90 cikin 100 na wutar lantarki daga hanyoyin makamashi da ake sabuntawa, da kuma Morocco wadda ke ci gaba da fadada shirye-shiryen samar da layin wutar lantarki na ƙarƙashin ruwa zuwa Turai.
Ya ƙara ba da misali da Tunisiya wadda ke gogayya da duniya a fannin fasahar zamani ta AI da kuma Rwanda wadda ke haɓaka jiragen sama marasa matuƙa a ƙasar.
Ba da lamuni mai rangwame, alkawuran yanayi
Guterres ya bukaci bankunan ci gaba a bangarori daban-daban da su ƙara rangwame kan lamunin da suke samarwa da daidaita alkawuran yanayi da kuma hanyoyin samar da jari ga 'yan kasuwa mata, wadanda ke wakiltar fiye da rabin masu kasuwanci na nahiyar.
A yayin da yake danganta ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya mai dorewa, babban jami'in na MDD ya yaba da koƙarin shiga tsakani da Afirka ke jagoranta a rikicin yankin, ciki har da na Habasha da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, yana mai jaddada cewa ci gaba mai dorewa ba zai taba wanzuwa ba tare da kwanciyar hankali na siyasa ba.


















