Turkiyya ta tura jiragen yaƙi na F-16 shida Arewacin Cyprus yayin yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran

Turkiyya ta aika jiragen yaƙi da kayayyakin kariya na sararin samaniya domin ƙara ƙarfafa tsaro a Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya a daidai lokacin da ake samun ƙarin fargaba da barazana saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya.

By
Turkiyya ta aika F-16 guda shida a Arewacin Cyprus don inganta tsaron TRNC. / AA

Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta tabbatar da tura jiragen yaƙi samfarin F-16 guda shida da kuma tsarin kariyar sararin samaniya zuwa Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya wato TRNC.

Wannan matakin wani ɓangare ne na shirin ƙarfafa tsaro a matakai daban-daban ga TRNC a daidai lokacin da ake yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

Ma'aikatar ta ce tura dakarun ne don "la'akari da sabbin abubuwan da suka faru a yankinmu," tare da cewa za a ɗauki ƙarin matakai idan aka ga ya zama dole dangane da abin da zai biyo baya.

Sanarwar ta jaddada niyyar ƙarfafa tsaron al'ummar 'yan Cyprus na Turkiyya a yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a yankin.

"Za a ci gaba da ɗaukar ƙarin matakai bisa ga ƙarin abubuwan da suka faru, idan an ga ya zama dole," in ji Ma'aikatar Tsaron.

Matakin ya biyo bayan rahotannin ƙaruwar fargaba a Gabashin Bahar Rum, wanda aka danganta da yaƙin da ke ci gaba tsakanin Isra'ila da Amurka kan Iran da kuma haɗarin bazuwar rikicin, ciki har da harba wani makami daga Iran kwanan nan wanda aka dakatar kafin ya shiga sararin samaniyar Turkiyya.

Tsibirin Cyprus na ɗauke da wani sansanin soja na Birtaniya.

TRNC, wadda aka kafa a 1983 kuma Turkiyya ta amince da ita, ta daɗe tana karɓar sojojin Turkiyya a matsayin mai tsaya mata bayan yarjejeniyar da aka cimmawa ta 1960.