| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
EFCC ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun
A cewar EFCC, jami’an hukumar na ofishin shiyyarta na Lagos Zonal Directorate 2 ne suka gudanar da samamen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da gudanar da sa ido.
EFCC ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun
EFCC ta cafke ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta Nijeriya (EFCC) ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya guda ɗaya a masana’antun sarrafa lithium guda huɗu da ke yankin Ogere a Jihar Ogun.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a yau.

A cewar EFCC, jami’an hukumar na ofishin shiyyarta na Lagos Zonal Directorate 2 ne suka gudanar da samamen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da gudanar da sa ido.

Hukumar ta ce jami’anta sun kwato buhunan duwatsun lithium, wayoyin hannu guda 18, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda huɗu, na’urorin karɓar tashoshin talabijin guda biyu, na’urar sarrafa talabijin da kuma motar dakon kaya kirar tirela daga wuraren.

EFCC ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Lithium na daga cikin muhimman ma’adanai da ake amfani da su wajen ƙera batir, ciki har da waɗanda ake amfani da su a motocin lantarki da na’urorin lantarki daban-daban.