| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
DSS ta gurfanar da mutum biyar gaban kotu bisa zarginsu da garkuwa da 'yan NYSC 20 a Imo
Daga bayan suka rage kuɗin fansan zuwa naira miliyan biyar kan ko wane mutum, lamarin da ya mayar da jumullar kuɗin naira miliyan 100 kan dukkan masu yi wa ƙasa hidima 20 ɗin.
DSS ta gurfanar da mutum biyar gaban kotu bisa zarginsu da garkuwa da 'yan NYSC 20 a Imo
A babbar kotun jihar Imo ake sauraran ƙarar da hukumar DSS ta shigar da waɗanda ake zargi da kasancewa masu garkuwa da mutanen

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gurfanar da mutum biyar da ake zargi da hannu a garkuwa da masu yi wa ƙasa hidima (‘yan NYSC) 20 tare da wani farin hula ɗaya a kan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha a jihar Imo.

A babbar kotun jihar da ke Owerri ne ake sauraron ƙarar bayan ‘yansanda sun kama waɗanda ake zargin yayin wani samame da aka yi bisa bayanan sirri a jihohin Ribas da Abia tsakanin 10 zuwa 14 ga watan Oktoba.

An yi garkuwa da masu yi wa ƙasa hidiman ne a cikin sanyin safiyar ranar 1 ga watan Oktoba bayan ‘yanbindiga sun far ma wata motar bas mai ɗauke mutum 18 da ke tafiya da fasinjoji daga Ibadan, babban birnin jihar Oyo, zuwa sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin Abia da Akwa Ibom, kuma suka kora su daji.

An kai harin ne kusa da Umunoha a ƙaramar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo da misalin ƙarfe 6:30 na safiya.

A wancan lokacin mai magana da yawun rundunar ‘yansanadan jihar Imo, Henry Okoye, ya ce an ceto 10 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin nan take, yayin da ake ci gaba da aikin bincike da ceto don gano waɗanda aka yi awon gaba da su.

Garkuwa da masu yi wa ƙasa hidiman ya ƙara jan hankalin jama’ar ƙasar bayan masu garkuwa da mutane sun tuntuɓi iyalan waɗanda aka sata suna neman kuɗin fansa da ya kai naira biliyan daya, inda suka ba su sa’o’i 24 su biya kudin.

Daga bayan suka rage kuɗin fansan zuwa naira miliyan biyar kan ko wane mutum, lamarin da ya mayar da jumullar kuɗin naira miliyan 100 kan dukkan masu yi wa ƙasa hidiman 20.

A ranar 7 ga watan Oktoba, wata runduna ta haɗin gwiwa ta jami’an DSS da sojoji da ‘yansanda sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin a cikin dajin Amakohia-Ubi a jihar Imo bayan bincike babu ƙaƙƙautawa. Daga baya aka yi wa waɗanda aka sata din magani.

Mayar da kuɗin fansa

Sai dai kuma, Alirat Wahab, uwa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, ta bayyana wa News Central Television cewa iyalinta ya biya naira miliyan 6 domin fanso ɗanta, wani iƙirari da ya sha bamban da yadda jami’an tsaro suka bayyana ceto masu yi wa ƙasa hidiman.

Wahab da mijinta, Obasanjo, daga bayan sun bayyana cewa an mayar musu da kuɗin da iyalinsu ya tara kuɗin fansan

Biyo bayan ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, jami’an tsaro sun ci gaba da ƙoƙarin gano da kuma kama waɗanda suka kai harin.

An kama mutum biyar da ake zargi da hannun aikata laifin yayin wasu jerin samame da aka yi a Port Harcourt, jihar Ribas da Aba, jihar Abia, tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan Oktoba.

Aikin ya haɗa da wata runduna ta haɗin gwiwa da hukumar DSS ta jagoranta, wadda ke aiki da jam’an soji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro.

Saura mutum uku da ake zargin sun tsere yayin samamen da raunin harbin bindiga in ji rahotanni.

Daga baya ne aka ƙaddamar da aikin neman su da sauran waɗanda da ake zargi da kasancewa cikin dabar garkuwa da mutanen.

 

Rumbun Labarai
An samu mutum 11,000 da ke fama da cutar tarin fuka a Jihar Filaton Nijeriya
Sojojin Nijeriya takwas sun rasu bayan motarsu ta taka nakiyar da aka dasa a kan titi
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanbindiga a Kano tare da ƙwato kudin fansa
An sauke DPO kan zargin 'yan kungiyar asiri sun gyara ofishin 'yansanda a Nijeriya
Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC)
Kansar mahaifa ta kashe mutum 7,093 cikin shekara ɗaya a Nijeriya: Gwamnati
Simon Ekpa: An rage ɗaurin da aka yi wa shugaban 'yan a-waren Biafra a Finland
Jihohi 12 da Tinubu zai je yaƙin neman zaɓen Nijeriya na 2027
Tamowa ta ƙaru a arewa maso gabashin Nijeriya da kaso 18 cikin 100, in ji Red Cross
’Yanta’addan Boko Haram sun kashe sojoji 10 a harin da suka kai wani sansanin soji a Nijeriya
Zaɓen Nijeriya na 2027: Ba ko ina zan bi tawagar yaƙin neman zaɓen APC ba – Tinubu
IMF ya gargaɗi Nijeriya kan mayar da tallafin man fetur
Cocin Katolika a Nijeriya ta rufe makarantu da asibitinta a jihar Benue saboda matsalar tsaro
NDLEA ta kama mutum 1,860, ta ƙwace tan 5.4 na miyagun ƙwayoyi a Kano
INEC ta yi ƙarin haske kan cire sunayen wasu ‘yantakarar gwamna a zaɓen 2027
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yanta'addan ISWAP fiye da 40 a Jihar Borno
Pantami ya bai wa INEC wa’adin kwana biyu ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe
'Yanbindiga sun kashe mutane 24 a sabbin hare-haren da suka kai a Nijeriya
Rahoton Bankin Duniya ya nuna ci gaba a sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya: Tinubu
Hukumar NDLEA ta sake kama wata tsohuwa mai shekara 83 kan zargin safarar miyagun kwayoyi