Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da aikin naira biliyan 137 na gyaran hanyar Bama zuwa Banki da kuma hanyar Dikwa zuwa Gamboru–Ngala a jihar Borno.
Wajen aikin yana arewa maso gabashin Nijeriya a jihar Borno kuma yana kusa da kan iyakar ƙasar da Jamhuriyar Kamaru, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwato.
A halin yanzu hanya ce ɗaya mai layi biyu da ke da tsawon kilomita 49.15km kuma ya taso ne daga garin Bama zuwa kan iyakar ƙasar da Kamaru .
Ministan ayyuka , David Umahi, ya ce Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai kammala aikin.
Umahi ya ce hanyar, da aka yi da zummar tsare da kuma sake haɗa hanyar arewa maso gabashin ƙasar da ta fi karkata kan kasuwanci, za ta haɓaka noma da kuma farfaɗo da harkoki bayan tayar da ƙayar baya a arewa maso gabashin ƙasar.
“Shi (Shugaban) wani babban mai tunani ne kuma wani mutum ne wanda ya shirya domin yin abin da ba za a iya tunani ba . A ƙarƙashin kulawarsa, waɗannan ayyukan za su kasance kamallalu,” a cewar Umahi.
Umahi ya bayyana cewa ayyukan, da aka fara bayar da su a shekarar 2021 kan kudin da ya fi naira biliyan 55, a halin yanzu ya kai abin da ya ɗara naira biliyan 70 da kuma naira biliyan 67, wani mataki na farko na hanyoyin Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru.
Da yake ƙaddamar da fara aikin a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataiamakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ce hanyoyin za su dawo da iya-tafiya da kuma farfaɗo da harkokin kasuwanci a yankin.
Ya kuma ce hanyoyin za su faɗaɗa iya inda hukumomin tsaro za su iya kaiwa da sake haɗa al’ummomin da suka shafe shekaru suna fama da shekarun rashin tsaro da rashin ababen more rayuwa.
“Hanyoyi jijiyoyin rayuwa ne na harkokin kasuwanci. Su suke tabbatar da ko manomi zai iya kai ga kasuwa ko ɗan kasuwa zai kai ga mai saya ko kuma yaro zai kai ga makaranta ko mara lafiya zai kai ga samun magani kuma ko hukumomin tsaro za su kai ga al’ummomi cikin lokaci,” in ji shi.
Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya mayar da ababen more rayuwa abin da ya fi mayar da hankali a kai saboda gurɓatattun hanyoyi suna ƙaƙaba matsi kan gidaje da kamfanoni da al’ummomi .
Ya bayyana cewa hanyoyi mara kyau suna rage gudun kasuwanci da ƙara tsadar abinci da ƙadaita al’ummomi da hana zuba jari da kuma raunata ƙarfin tattalin arzikin al’ummomin karkara.
Ya kuma bayyana cewa a wani yanki da ke kan farfaɗowa daga tasirin tayar da ƙayar baya, dole a kalli gyara hanya a matsayin aikin tattalin arziki da na tsaro.
Shettima ya ce hanyoyin da suka ɓaci suna sa tafiya yana wahala da kuma taƙaita ikon sintiri na jami’an tsaro da kare mutane da kuma kai ɗauki cikin hanzari.
“Hanyoyi mara kyau suma haɗarin tsaro ne . Wata hanyar da ke da wahala ‘yan ƙasa su iya tafiya a kansa ita ma tana da wahala ga jami’an tsaro su yi sintiri da kuma kare [mutane],” in ji shi.
Ya bayyana hanyar Bama zuwa Banki a matsayar wata hanya mai ɗaukar “nauyi mai muhimmanci ,” yana mai ƙarawa da cewa hanyar Dikwa zuwa Gamboru-Ngala wani ɓangare ne na tunani ɗaya na sake haɗa al’ummomi .
Daga farko , Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote da ‘yankwangilan da ke aikin, sun ce rukunin kamfanoninsa na da manyan hanyoyi 12 da suka kai fiye da kilomita 1,000 a sassan yakunnan siyasar ƙasar shida.
Dangote ya ce ayyukan idan aka haɗa su za su raba gwamnatin Nijeriya da naira tiriliyan uku a ƙarƙashin tsarin bashin haraji gwamnatin tarayya na gina hanyoyi.
Ya bayyana cewa hanyar Bama zuwa Banki , da kuma Dikwa zuwa Gamboru-Ngala za su buɗe tattalin arzikin Nijeriya da taimaka wa ayyukan soji kana su inganta tsaro da kuma janyo hankalin masu zuba jari.
A jawabinsa , Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya kuma ce ayyukan suna da muhimmanci ga ƙoƙari farfaɗo da lammura na jihar , yana mai ƙarawa da cewa hanyoyin za su faɗaɗa harkokin kasuwanci zuwa Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.









