| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan
Turkiya ta ce za ta ci gaba da magana a kan Netanyahu da abokansa kuma za ta bi hanyoyin shari'a na duniya don samun amincewa.
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausar suka kan abin da ta bayyana a matsayin “zarge-zarge marasa tushe, na tsokana kuma marasa gaskiya” da aka yi wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan, tana mai cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na ƙoƙarin yaudarar ra’ayin jama’ar duniya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Laraba, ta ce zarge-zargen da aka yi wa Erdogan wani yunƙuri ne daga Netanyahu da na kusa da shi na karkatar da hankalin duniya daga ayyukansu.

“Waɗannan zarge-zarge marasa tushe, na tsokana kuma na ƙarya da aka yi wa Shugabanmu mai girma ba komai ba ne illa wani yunƙuri na Netanyahu da abokan tafiyarsa na yaudarar ra’ayin jama’ar duniya,” in ji sanarwar.

Ma’aikatar ta kuma ce “ƙaryar da Netanyahu, wanda ta kira ƙwararren mai aikata kisan kiyashi, ke amfani da ita domin ɓoye gaskiya ba za ta iya kawar da alhakinsa kan manyan laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba.”

Ta jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da bayyana abin da take kira gaskiya game da Netanyahu da waɗanda ke tare da shi, tare da neman a hukunta su ta hanyoyin shari’a na ƙasa da ƙasa.

“A matsayinmu na Turkiyya, za mu ci gaba da bayyana gaskiyar da ta shafi Netanyahu da abokan aikinsa ba tare da wata-wata ba. Haka kuma za mu ci gaba da ƙoƙarin ganin an gurfanar da su a gaban kotunan ƙasa da ƙasa saboda ayyukan da suka saɓa wa doka da ƙa’idodin ɗan Adam,” in ji sanarwar.

A wani bangare kuma, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a ƙasashen Syria da Lebanon sun kai wani mataki da suke barazana ga Turkiyya ma.

Ya ce abin da ya kira “ta’addancin” Isra’ila na zama barazana ga duniya baki ɗaya, kuma wajibi ne a dakatar da shi.

Shugaban ya kuma yi magana kan abin da ya kira ruɗin samar da “Ƙasar Alkawari”na Isra’ila, yana mai cewa Turkiyya na sane da manufar da ke bayan hakan.

“Da yardar Allah, ba za mu taɓa bari hakan ya faru ba,” in ji Erdogan.

Rumbun Labarai
Taron Koli na NATO a Ankara na nuna muhimmiyar rawar Turkiyya a harkar tsaro da diflomasiyyar duniya
Muhimmin labarin fursunonin yaki Turkawa da ya sauya fasalin aƙidun horon sojojin NATO
Turai za ta yi amfani da taron NATO a Ankara ta nuna wa Trump kyakkyawar niyyarta kan tsaro: Jamus
Shugaban Turkiyya Erdogan ya karɓi baƙuncin Firaministan Pakistan Sharif a Istanbul
Salon Turkiyya na sasanci da taimakon tsaro yana inganta harkar tsaro a Afirka
Yadda Turkiyya ke ƙarfafa rawar da take takawa a NATO kafin babban taron ƙawance a Ankara
Shugaba Erdogan ya soki Isra'ila game da gangamin ɓata suna da ƙarairayi kan Turkiyya
Tawagar majalisar dokokin NATO ta ziyarci kamfanin Baykar mai ƙera jirage marasa matuƙa a Ankara
Taron NATO na Ankara zai kasance "babban dandali mai ƙarfi na musayar ƙwarewa: Erdogan na Turkiyya
Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya na neman a bunkasa kasuwanci a tsakanin duniyar Musulunci
Ma'aikatan agajin Turkiyya sun fara aikin ceto a Venezuela bayan girgizar ƙasa
Turkiyya ta tura tawagar bincike da ceto zuwa Venezuela bayan iftila'in tagwayen girgizar kasa
Shugaban Turkiyya da na Mauritaniya sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashensu da batutuwan yanki
'Ankara za ta ƙara ɗaukaka a diflomasiyyar duniya ta hanyar karbar tarukan NATO da ƙasashen Turkawa'
Turkiyya ta fitar da jirgin ruwan yaƙi na farko ga wata ƙasa memba a NATO da EU: Shugaba Erdogan
Ministan Tsaron Turkiyya ya ce taron NATO na Ankara zai zama muhimmin sauyi ga ƙawancen ƙungiyar
Hukumar leƙen asiri ta Turkiyya ta kama babban jagoran Daesh tare da dawo da shi ƙasar
Asibitin Turkiyya ya kafa 'tarihin' zama na farko a duniya da aka yi dashen hanta da ta haɗa mutum 8
Erdogan ya jinjina wa Turkiyya kan komawa Gasar Kofin Duniya bayan shekara 24
Turkiyya da Saudiyya sun sa hannu kan muhimman yarjejeniyoyi a fannin layin dogo da sufuri