| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Yarjejeniyar za ta bai wa kamfanonin Amurka muhimmiyar damar taka rawa a fannin haɓɓaka makamashin nukiliya na Saudiyya, tare da samar da damar bunƙasa sinadarin uranium na ƙasar.
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Trump ya gabatar da yarjejeniyar haɗin gwiwar nukiliya ta Saudiyya ga Majalisar Dokokin Amurka.

Shugaba Donald Trump ya gabatar da wata muhimmiyar yarjejeniya ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Dokokin Amurka don yin muhawara, a cewar Jaridar Wall Street Journal.

Jaridar ta ambato wani jami'in gudanarwa a gwamnatin Trump wanda ya bayyana cewa, shugaban bai yi watsi da buƙatarsa ​​kan Saudiyya ta daidaita dangantakarta da Isra'ila ba, sharaɗin da ya janyo cikas ga ƙoƙarin kammala gagarumar yarjejeniya da Riyadh.

A watan da ya wuce ne gwamnatin Trump ta sanar da ƙulla yarjejeniyar nukiliya ta shekaru 30 da Saudiyya.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, kamfanonin Amurka za su taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka kayayyakin more rayuwa na nukiliyar Saudiyya, tare da shirin da aka tsara don hana sauran kamfanonin ƙasashen waje shiga cikin yawancin ayyukan.

A ranar Litinin aka aika yarjejeniyar ga Majalisar Dokoki a hukumance kamar yadda dokar Amurka ta tanada, a cewar rahoton.

A yanzu ‘yan majalisar za su samu damar yin bita kan yarjejeniyar kuma wataƙila su yi ƙoƙarin hana ta rawar gani.

Majalisar za ta buƙaci wani kuduri na haɗin gwiwa da ke adawa da yarjejeniyar, yayin da a bangare guda 'yan majalisar dokokin za su buƙaci rinjaye da kashi biyu bisa uku daga dukkan majalisun ƙasar biyu domin kawar da yiwuwar kin amincewar shugaban ƙasa.