SIYASA
2 minti karatu
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a India
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a wani asibitin India, a cewar ‘yan sanda da hukumomin ƙasar.
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a India
Gwamnatin kasar Kenya ta tabbatar da mutuwar tsohon Shugaban Kasa, Raila Odinga
15 Oktoba 2025

Madugun ‘yan adawan Kenya kuma tsohon Firaministan ƙasar Raila Odinga ya mutu a India, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai a ƙasashe India da Kenya suka ruwaito daga majiyoyin asibiti da na ‘yan sanda.

Odinga, mai shekara 80, wanda ya je Koothattukulam a gundumar Ernakulam ta Kerala domin jinyar gargajiya mai suna Ayurve, ya mutu ranar Laraba sakamakon bugun zuciya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Press Trust na India ya ruwaito daga ‘yan sanda da hukumomin asibiti.

Kaasar Kenya ta tabbatar da mutuwar tasa a hukumance, inda gwamnati ta fitar da sanarwar rashin.

Odinga ya faɗi ne yayin irin tattakin nan na safiya a cikin wani asibitin gargarjiya na Ayurve, kuma nan take aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa a Koothattukulam, inda aka bayyana cewa ya mutu da misalin ƙarfe 9.52 na safiya, kamar yadda wani mai magana da yawun asibitin gargajiya na ido na Ayurve ya shaida wa Press Trust ta India.

Wasu shugabannin Afirka sun fara tura saƙonnin ta’aziyyarsu inda Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa shafinsa na X cewa: “A madadin gwamnatin Ethiopia, ina miƙa ta’aziyyata game da rasuwar tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga. Allah Ya sa ya huta.’’

‘Bugun zuciya’

Kafofin watsa labaran India sun ba da rahoton cewa Odinga, wanda yake jinya a birnin Kochi da ke kudancin India, ya samu bugun zuciya ranar Laraba  kuma aka garzaya da shi asibiti, inda aka bayyana cewa ya mutu.

A matsayinsa na jagoran ‘yan adawa, Odinga ya sha kaye a dukkan takarar shugaban ƙasa biyar da ya yi inda biyu daga cikin zaɓukan suka janyo rikici.

Aikinsa a matsayin mai gwagwarmayar dimokuraɗiyya cikin shekarun da suka wuce ya taimaka wajen samar da muhimman gyararraki biyu na ƙasar: dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da yawa a shekarar 1991 da kuma sabon kundin tsarin mulki a shekarar 2010.

Ya jagoranci jerin zanga-zanga bayan zaɓen 2007 mai cike da ce-ce-ku-ce da ya jefa ƙasar cikin rikici mafi muni tun bayan da ta samu ‘yancin kai. Kimanin mutum 1,300 ne aka kashe kuma aka raba dubban mutane da gidajensu.

Rumbun Labarai
Kutungwilar Netanyahu kan tsagaita wuta a Gaza ita ce ci gaba da kashe Falasdinawa
Zaben Tanzania: Intanet ya katse sannan zanga-zanga ta barke a ranar zabe
Masu nazarin kayan tarihi sun gano kisan gillar Faransa a wata makabartar Senegal
Mahama ya hana ministoci bayyana manufofin gwamnatin Ghana sai da izinin majalisar ministoci
Shugaban Sudan al Burhan ya ce ‘sojojin ƙasar sun janye’ daga Al Fasher
Hamas na aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta amma Isra'ila na ci gaba da karya ta, in ji Erdogan
Ghana tana alhinin mutuwar matar tsohon shugaban ƙasar, Nana Konadu Agyeman-Rawlings
Kotu a Bangladesh ta tura manyan hafsoshin soji gidan yari a wata shari’a ta tarihi
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman  gidan kaso kan karɓar kuɗin a wurin Gaddafi
Firaministan Falasɗinu ya bayyana shirin ware dala biliyan 65 don sake gina Gaza
Shugaban Madagascar na ɓuya a wani 'wuri mai aminci' bayan mummunar zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar
Yadda diflomasiyyar Erdogan na Turkiyya ta taimaka wajen cim ma tsagaita wuta a Gaza
Burkina Faso ta kama ma’aikatan jinƙai bisa zargin leƙen asiri
Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra’ila a Gaza: Yadda Amurka ke kare Netanyahu daga tuhuma
Swahili ne mafita ga Gabashin Afirka ba Faransanci ba
Za a ƙaddamar da shirin bayar da lasisin bindiga na intanet a Ghana
ICC: Yaudara daga wadanda suka kafa ta, mafaka ga mambobin ƙasashen Afirka
Fayyaceccen bayanin Erdogan a MDD: Gaza, 'ƙasar Isra'ila', da makomar yankin
Mene ne daftarin Babban Zauren MDD kan mafitar samar da ƙasashe biyu da ƙarara ya yi watsi da Hamas?
INEC ta buƙaci a hukunta duk wanda ya fara kamfen ɗin 2027 kafin lokaci