Ghana ta biya basussukan dala biliyan 1.47 na fannin makashi da ake bin ta
Ministan Kudi Forson ya ce fannin makamashin na cikin yanayi na rauni sosai a lokacin da Shugaba John Dramani Mahama ya karɓi ragamar mulki.
Ghana ta biya adadin jimillar dala biliyan 1.47 a shekarar 2025 don warware tsoffin basussukan da ake bin ta a fannin makamashi da kuma dawo da samun garanti na Bankin Duniya a wannan sashen, in ji Ma'aikatar Kudi a wata sanarwa a ranar Litinin.
A cewar Ministan Kudi Cassiel Ato Forson, gwamnati ta biya duka basussukan dala miliyan 597.15 miliyan, ciki har da kuɗin ruwa, wanda aka karba ƙarƙashin Garanti na Bankin Duniya (Partial Risk Guarantee), wanda aka yi amfani da kuɗaɗen a shekarun baya.
Wannan biyan ya dawo da garantin, wanda yake da muhimmanci ga amincewar masu zuba jari a bangaren wutar lantarki na Ghana.
Minista Forson, a cikin bayanin da ya wallafa a X, ya ce bangaren makamashi yana cikin mawuyacin hali lokacin da Shugaba John Dramani Mahama ya karbi mulki a watan Janairun 2025, bayan shekaru na rashin biyan kuɗi ga iskar gas da ake samarwa ga bangaren wutar lantarki.
“Lokacin da Shugaba Mahama ya karbi mulki a watan Janairu 2025, an tilasta bangaren makamashi zuwa durƙushewa saboda shekaru da aka shafe na rashin biyan kuɗi ga gas ɗin da ake samarwa ga bangaren wutar lantarki daga bangaren Offshore Cape Three Points (OCTP).
“Saboda haka, an biya Garanti na Bankin Duniya na dala miliyan 500 miliyan gaba ɗaya wanda aka ciyo a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata,” in ji Forson.
'Iyakance taruwar bashi'
Haka zalika an bayyana cewa gwamnati ta biya takardun biyan gas da suka rage na kimanin dala miliyan 480 da ake bin ENI da Vitol saboda samar da wutar lantarki daga filin Offshore Cape Three Points (OCTP).
“Gwamnatin Ghana na tabbatar wa al'umma baki ɗaya, masu ruwa da tsaki a masana'antu, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa cewa zamanin tara bashi da ƙin biyansa a bangaren makamashi ya ƙare,” in ji Forson.
Gwamnatin ta kuma biya kusan dala miliyan 393 a matsayin tsoffin basussukan da ake bin masu samar da wuta masu zaman kansu (IPPs), wanda hakan ya ƙara daidaita sashen.