| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Tiger Woods ya lashe manyan kofunan wasan golf har 15, amma ranar 31 ga Maris ya sanar da cewa zai janye daga wasan golf na "tsawon lokaci don neman magani da mayar da hankali kan lafiyarsa."
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Shekarun Tiger Woods 50 a duniya

Wata kotu a Florida ta Amurka ta soke lasisin tuƙin mota na shahararren ɗanwasan golf, Tiger Woods, wanda zai hana shi tuƙi tsawon shekaru biyar.

Ranar Laraba ne ɗanwasan ya amsa wasu daga cikin laifukan da ‘yansanda suka tuhume shi, bayan yarjejeniyar amsa laifi don sassaucin hukunci a kotu.

Kotun Martin County Circuit da ke jihar Florida ta kuma ɗora masa tarar dala $1,500, bayan an tuhume shi da laifin tuƙin ganganci da ƙin amincewa da a yi masa gwajin maye bisa doka.

Mai shekaru 50 a duniya, Tiger Woods ya iso kotu ne tare da budurwarsa, Vanessa Trump da kuma lauyansa, Doug Duncan.

Tun ranar 27 ga Maris ne aka kama Woods kan zargin tuƙi cikin maye da kuma ƙin amincewa da umarnin doka, bayan motarsa ta gogi wata tirela da ake ja, har ta kai motar tasa ta gangara a tuntsure.

Da fari, Woods ya ƙi amincewa ya amsa zarge-zargen da aka masa, inda ya shaida wa hukumomi cewa kansa yana ƙasa yana kallon wayarsa kuma yana canja tashar rediyo, wanda ya sa bai ga motar gabansa ta rage gudu ba.

Sai dai jami’an ‘yansandan da suka isa wajen hatsarin sun ce sun tarar da shi yana “gumi kashirɓan” kuma yana motsawa "ba karsashi kuma salo-salo" sanda ake masa intabiyu.

Sai dai gwajin numfashin bakinsa bai nuna akwai barasa a jinisa ba. Amma kuma ya ƙi amincewa a masa gwajin fitsari ko na jini don fayyace ko ya sha ƙwayoyi.

Rayuwar wasa

‘Yansandan sun ce sun gano ƙwayoyi biyu na hydrocodone a aljihun wandonsa, kuma masu gabatar da ƙara sun samu bayani kan ƙwayoyin da likitoci suka rubuta masa.

A rayuwarsa ta wasa, Tiger Woods ya lashe kofunan wasan golf har 15, amma ranar 31 ga Maris ya sanar da cewa zai janye daga wasan golf na "tsawon lokaci don neman magani da mayar da hankali kan lafiyarsa."

Kuma ya kashe makonni da dama a wata cibiyar marasa lafiya a Switzerland.

Ko a 2017, an taɓa kama Woods kan zargin tuƙi cikin maye, bayan ‘yansanda sun same shi yana barci yayin da yake tuƙi a mota, wadda take da fasassun taya biyu kuma bambar gaba da ta baya a a lalace.

A lokacin Woods ya ce ya sha nau’o’in maganin kashe ciwo. Daga bisani ya amsa laifin tuƙin ganganci sanda ya amince ya shiga shirin maganin a cibiyar magance jarabar shan ƙwaya matsala a shekarar.

A Fabrairun 2021, Woods ya samu munanan raunuka a ƙafa a hatsarin mota guda a wajen Los Angeles, inda motarsa ƙirar SUV mirgina sau da yawa sannan Woods ya maƙale a ciki.

Haka na, an yi masa tiyata a ƙafarsa ta dama, inda har aka saka masa rodi a kashin ƙafa, kuma ya yi zaman asibiti na watanni uku.

Sakamakon, gasar da Tiger Woods ya shiga babbar gasar PGA ta ƙarshe tun a Yulin 2024. A yanzu an shirya zai karɓi baƙi a gasar Hero World Challenge a ƙasar Bahamas a ranakun 3-6 na Disamba.

Rumbun Labarai
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Shugaban hukumar ƙwallo da kocin Portugal sun zauna don lallashin Ronaldo bayan ƙin saka shi a wasa
Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia
An samu Manchester City da laifin keta dokokin kuɗi
Nijeriya da Ghana sun sha kashi a wasannin neman gurbin shiga Gasar AFCON ta 2027
Manyan kulob sun shirya wawason 'yanwasan Man City idan kotu ta kore ta daga Gasar Firimiya
Zidane ya yaba wa Turkiyya gabannin wasansa na farko a matsayin mai horar da tawagar Faransa
Taiwo ya maye gurbin Osimhen yayin da aka buɗe sansanin horaswa na Super Eagles
Kocin Super Eagles ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wasanni a Satumba da Oktoba
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa