| Hausa
KASUWANCI
2 minti karatu
Ghana ta bai wa wani kamfanin ƙasar lasisin haƙar zinare kan $1bn
Ghana ta zabi kamfanin ayyukan haƙar ma'adinai na gida wato Engineers & Planners Ltd don ya karɓi ragamar aikin hako ma'adinan zinare daga hannun Gold Fields na Damang, a cewar ministan ma’adinai na ƙasar a ranar Talata.
Ghana ta bai wa wani kamfanin ƙasar lasisin haƙar zinare kan $1bn
A baya kamfanin ma'adinai na Gold Fields da zama a Afirka ta Kudu ne ke gudanar da aikin hakar zinare na Damang a Ghana. / Reuters
8 Afrilu 2026

Gwamnatin Ghana ta zaɓi kamfanin haƙar ma’adinai na cikin gida wato Engineers & Planners Ltd don maye gurɓin ayyukan Glod Field na hakar zinare, kamar yadda ministan harkokin ma’adinai na ƙasar ya bayyana a ranar Talata.

Ghana, wacce ke ƙoƙarin haɓaka ayyukan kamfanonin cikin gida a fannin haƙar ma'adinai, ta ƙi amincewa da tayin sabunta kwangilar kamfanin Gold Fields wanda ke Johannesburg kana ta karɓe ikon ayyukan kamfanin a bara, inda ta dakatar da yarjejeniyar tsawon shekaru da ke tsakaninsu.

Daga nan sai ta fara tantance tayin kamfanonin cikin gida don farfaɗo da ɓangaren kan dala biliyan 1.

A wata sanarwa da aka fitar Emmanuel Armah Kofi Buah ya ce hukumar da ke sa ido kan harkokin hakar ma'adinai ta cim ma yarjejeniya da kamfanin E&P.

Rawar kamfanonin cikin gida a fannin haƙar ma'adinai na Ghana

Kamfanin ya nuna cewa yana da tsabar kuɗi da ya kai dala miliyan 505, matakin da ya cika sharuɗɗan gwamnati na cewa dole sai duk wani kamfani ya mallaki aƙalla dala miliyan 500 kafin ya samu wannan dama.

Kazalika kamfanin ya samu maki mai yawa a fannin ƙwarewa da kayan aiki, tsaro da aminci da kuma mallakar sauran abubuwan cikin gida, in ji sanarwar.

Da farko kamfanin Gold Fields, wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana gudanar da ayyukan hakar ma’adinai a Damang, ya bayyana cewa zai sayar da wurin, yana mai nuni kan ƙarancin albarkatu da kuma rashin tanadi na tattalin arziki.

A watan jiya ne kamfanin ya bayyana cewa, yana ƙoƙarin tabbatar an miƙa wurin ga wani sabon kamfani ba tare da tsaiko ba.

Hukumomin sun ce yarjejeniyar tana da nufin tabbatar da ci gaba da haƙar ma'adinan, tare da kare ayyukan yi da kuma ƙara yawan masu zuba jari a fannin haƙar ma'adinai na Ghana.