| Hausa
DUNIYA
1 minti karatu
Fafaroma ya yi kira a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gabar Yamma
Fafaroma ya yi kira ga kasashen duniya su tabbatar da samar da kasashe biyu masu 'yancin gashin kansu domin 'adalci da dawwamammen zaman lafiya’.
Fafaroma ya yi kira a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gabar Yamma
Fafaroma Leo ya jagoranci addu’ar Angelus a Piazza della Liberta da ke Castel Gandolfo, kusa da Rome, Italiya, ranar 16 ga Agustan 2026. / Reuters

Fafaroma Leo XIV ranar Lahadi ya jaddada kira a kawo karshen cin zarafin da Isra’ila take yi wa Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan sannan ya nemi kasashen duniya su tabbatar da ganin an samu kasashe biyu masu 'yancin kansu.

Yayin da yake jawabi a wurin taron addu’ar mako-mako ta Angelus, Leo ya yi kira a kawo karshen “cin zarafin da ake ta yi wa al’ummar Falasdinu a Gabar Yammacin Kogin Jordan”, a cewar Vatican News.

Kazalika ya yi kiran gaggawa ga kasashen duniya su “tabbatar da an samu ci gaba wajen samar da kasashe biyu masu ‘yancin kansu, domin adalci da dawwamammen zaman lafiya”.

Fadar Vatican ta sha nanata cewa samar da kasashe biyu masu ‘yancin kansu kamar yadda dokokin kasashen duniya suka tanada ita ce hanya kadai ta samun dawwamammen zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Har wa yau Fafaroma ya bude bikin Wasannin Mediterranea a birnin Taranto na kudancin Italiya, inda ya yi fatan ganin wasannin sun kasance wata “alama ta zaman lafiya da zumunta tsakanin al’ummomin wannan yankin da sauran kasashen duniya”.

‘Yanwasa daga nahiyar Afirka da Asia da Turai da ke kusa da Tekun `Mediterranea ne suke fafatawa a gasar.