Shirin kawar da shara na Matar Shugaban Turkiyya ya tsara taswirar Ankara na karbar bakuncin COP31

Yayin da Turkiyya ta shirya karɓar bakuncin babban taron sauyin yanayi na duniya na 2026, gagarumin shirin Matar Shugaban Ƙasar ya tashi daga matakin fafutuka zuwa ga tsarin kula da yanayi na duniya.

By
Shirin Zero Waste ya bayyana dadadden fafutukar Emine Erdogan na kawar da sharar a matsayin mafita mai amfani ga ƙalubalen muhalli. / AA

Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta sanya shirin ƙasar na kawar da shara a kan gaba a shirye-shiryen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 31 (COP31).

La’akari da tushen gidauniyar kan muhalli a Istanbul yake, za ta zama jagora wacce za ta kaddamar da cikakken tsarin shirin mai dorewa ga taron.

Tsarin, wanda Gidauniyar Zero Waste ta shirya, ya bayyana yadda taron COP31 zai mayar da hankali wajen rage hayakin carbon, inganta amfani da albarkatu tare da sanya ayyukan da suka shafi muhalli a dukkan fannoni na taron, tun daga jigilar kayayyaki da wuraren da za a gudanar da tarurruka na masu ruwa da tsaki da kuma bayyana gaskiya.

COP31, wanda a bana Turkiyya ce za ta jagoranta kuma ta karɓi bakuncinsa a watan Nuwamba na 2026, ana sa ran zai tattaro kusan ƙasashe 200 don tattaunawa kan babi na gaba na matakin da za a ɗauka wajen magance sauyin yanayi na duniya ƙarƙashin Yarjejeniyar Paris.

Tsarin COP31 mai dorewa ya samar da taswirar hanyoyin da duniya za ta bi waɗanda suka haɗa da ka'idojin sarrafa sharar gida, da dabarun rage gurɓatacciyar iska da samar da dabaru, da tsarin sufuri mai ɗorewa da tsre-tsren ayyuka tare da samar da yanayin muhalli mai kyau da za a gudanar da tarurrruka.

Haka nan ya tsara hanyoyin tabbatar da riƙon amana da gaskiya tsakanin dukkan mahalarta.

Ɗaɗaɗɗen fafutukar matar shugaban ƙasa

Wannan shiri ya nuna ɗaɗaɗɗen fafutukar Emine Erdogan kan kawar da shara a matsayin mafita mai amfani kana mai araha ga ƙalubalen muhalli.

A ƙarƙashin jagorancinta, gagamin shirin ‘Zero Waste’ ya samo asali daga manufofin ƙasa zuwa tsarin da aka amince da shi a duniya don ɗorewa.

Baya ga tsare-tsaren fasaha, gidauniyar tana gina tsari mai girma da shirye-shirye masu ruwa da tsaki ya yawa a faɗin Turkiyya.

Daga ciki har haɗin gwiwa da jami'o'i da cibiyoyin bincike kan haɓaka manufofi, da haɗin gwiwa da gwamnatocin ƙananan hukumomi kan ayyukan birane masu ɗorewa, da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu don haɓaka samfuran samar da ƙarancin gurɓataccen iska da kuma wayar da kan jama'a.

Shugaban Gidauniyar Zero Waste Samed Agirbas ya ce, a yanzu ba a daukar shirin a matsayin manufa ta muhalli kawai amma a matsayin wata mafita mai ma'ana da za a iya aunawa a yaƙi da sauyin yanayi.

Ya bayyana COP31 a matsayin wata dama ta tarihi da za a gabatar da tsarin Turkiyya na kawar da shara ga al'ummar duniya a wani babban mataki.

Diflomasiyyar Muhalli

A yan’shekarun nan rawar da Emine Erdogan ke takawa a fannin diflomasiyyar muhalli ta duniya ya karu sosai.

Wani kuɗurin Majalisar Dinkin Duniya na watan Disamban 2022 da Turkiyya ta jagoranta kana kasashe 105 suka dauki nauyinsa ya ayyana ranar 30 ga Maris a matsayin Ranar kawar da shara ta Duniya.

Kazalika Erdogan ya gabatar da jawabi na farko a taron farko na watan Maris na 2023 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

A yayin wannan taron, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da kafa Kwamitin Ba da Shawara na Manyan Mutane kan shirin kawar da shara sannan ya buƙaci Erdogan da ta zama shugabar kwamitin, rawar da ta karɓa hannu biyu.

Daga baya ta jagoranci wani babban taro mai taken "Zuwa ga Ƙungiyar Kawar da Shara ta Duniya" a ginin Turkiyya da ke New York, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya zama na farko da ya sanya hannu kan samar shirin kawar da shara ta Duniya.

Za a gudanar da taron COP31 ne daga ranar 9 zuwa 20 ga Nuwamba, 2026, musamman a birnin Antalya da ke yankin Bahar Rum, yayin da aka shirya taron shugabannin a Istanbul.

Ana sa ran tattaunawa za ta mayar da hankali kan sabbin manufofin kawar da hayaki mai gurbata muhalli, da dabarun daidaitawa, da kuɗaɗen yanayi da aiwatar da kasuwannin hayakin carbon na duniya.

Ta hanyar sanya shirye-shiryen COP31 a cikin tsarin kawar da shara na ‘Zero Waste’ wanda matar shugaban ƙasa ke jagoranta, Turkiyya ta kuduri aniyya haɗa ƙwarewarta ta diflomasiyya da jagoranci na muhalli, ta hanya sanya dorewa ba kawai a matsayin jigon taro ba amma a matsayin wata ƙa'ida da ke jagorantar taron.