| Hausa
TURKIYYA
6 minti karatu
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Shugaban Turkiyya, a wata maƙala a kafar Bloomberg, ya ce dole kwamitin ya iya nuna haƙiƙanin duniya na yau, yana mai ba da shawarar cewa ya kamata a babban zauren MƊD ya samu ƙarin iko da kuma kawo ƙarshen ikon hawa kujerar naƙi.
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Toshon Hoto: Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a lokacin da yake halartar wani taron manema labarai a Ankara.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga a cikakkiyar gyara ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ciki har da cire ikonn hawa kujerar naƙi mambobin kwamitin na din din din, yana mai cewa dole tsarin ƙasa da ƙasa ya nuna haƙiƙanin abin da ke faruwa a duniya a yau.

A wata maƙala ga Bloomberg mai taken "Ya kamata MƊD ta soke Ikon Hawa Kujejar Na-ƙi na Kwamitin Tsaro", Erdogan ya ce rike-rikecen na kwanan nan, ciki har da annoba masu yaɗuwa a duniya da girgiza na makamashi da katse hanyoyin samun abubuwa da kuma rikce rikice na yanki, sun nuna iyakar barin mafita ta ƙalubalen duniya a hannun matakan wasu ‘yan ƙasashe kaɗan.

Yana mai jaddada cewa dole tsare-tsaren cim ma matsaya na duniya su sauya kamar yadda yanayin yau yake, ya ce Kwamitin Tsaro na MƊD na ci gaba da nuna tsarin da aka kafa bayan Yaƙin Duniya na II.

Erdogan ya ce ana buƙatar wani tsarin wakilci "da ya fi aiki da adalci da kuma riƙon gaskiya" kuma ya yi kira da faɗaɗa yadda shigar ƙasashen duniya waje yadda duniya ke cim ma matsaya.

Ya ce ya kamata a fahimci kirar Turkiyya cewa "Duniya ta fi biyar " a matsayin jan hankali na faɗaɗa rarraba nauyi da ayyuka a tsarin ƙasa da ƙasa.

Erdogan ya daɗe yana neman gyare-gyare kan MƊD, yana mai yawan amfani da taken : “Duniya ta fi biyar,” wanda ke nufin mambobin Kwamitin Tsaro na MƊD.

"Yana da muhimmanci a sauya buƙatar gyaran a cikin wata taswirar hanya a aikace," in ji Erdogan. "A tsakiyar wannan tsawirar hanyar nan ya kamata a saka soke ikon hawa kujerar naƙi."

Ƙara sabbin mambobi na din din din kawai a cikin Kwamitin Tsraon MƊD ba zai warware matsalar taruwar ikon yanke hukunci zuwa a hannun wasu ‘yan ƙasashe kaɗan ba.

Miamakon hakan ya kamata gyara ya kasance kan tsarin cewa babu ƙasar da za ta samu iko na din din din na iya hana muradin mafi yawa na ƙasashen duniya ba, a cewarsa.

'Ƙarin damar taka rawa ga Babban Zauren MƊD'

Shugaban ya kuma yi kira da a samu sabon daidaito tsakanin Kwamitin Tsaro na MƊD da Babban Zauren MƊD.

Ya ba da shawarar ƙarfafa ikon Babban Zauren MƊD ba tare da mambobi na dindindin ba, inda ƙasashe na Babban Zauren MƊD za su rinƙa zaɓen mambobin kan ƙayyadadden wa’adi.

A ƙarƙashin wannan tsarin da Erdogan ya zayyana, ƙasashe da ke neman ƙrin wa’adi za su buƙaci sake samun yardar yawancin ƙasashen Babban Zauren MƊD ta hnayar zaɓuka.

"Ya kamata a ƙarfafa wakilci da riƙon gaskiya na Kwamitin Tsaro na MƊD a gaban Babban Zauren MƊD," in ji shi.

Ya ce tsarin ƙasa da ƙasa na gaba ba za a iya gina shi ba ta hanyar kare matakan matsayin ƙasashe na baya.

"Abubuwan da suka faru a cikin kwatan karni ɗaya da ya gabata —wanda lokaci ne mai gajeren zango idan aka kwatanta da tarihin dan adam—sun nuna cewa babu wani tsarin daidaiton iko ko tsarin duniya da ke dawwama," in ji shi.

Erdogan ya bayyana cewa sabbin cibiyoyin iko sun bayyana a fannoni daban-daban, tun daga tattalin arziki da tsaro har zuwa fasaha da huldar diflomasiyya, yayin da hukumomin kasa da kasa suka gaza daidaito da waɗannan sauye-sauye cikin sauri yadda ya dace.

Ya kara da cewa yake-yake da rikicin sauyin yanayi da kwarar ‘yan ci-rani ba bisa ka'ida ba da kuma raunin tattalin arziki sun jaddada muhimmancin samun hukumomi masu karfi da tattalin arziki mai jure kalubale da kuma karfin tsaro mai inganci.

Shugaban kasar Turkiyya ya yi nuni da karuwar muhimmancin hanyoyin kasuwanci da dabaru da sufuri da makamashi wadanda ke da tsaro da kuma ɗorewa.

Erdogan ya bayyana cewa karfin tattalin arzikin Asiya na karuwa, yayin da kasashen Afirka ke neman samun wakilci mai karfi da ya dace da damar da nahiyar ke da ita.

Kira ga ƙarin adalci a tattalin arzikin duniya

Ya kuma ƙara da cewa ƙasashe masu tasowa suna bayyana abin da suka fi bai wa fifiko kuma ya ce matsaloli na yanki ba za a iya warware su ba ta hanyoyin da aka tsara daga waje.

"Matakan da suka dogara kan manufofin ƙasashen da abin ya shafa, yanayin da yankunansu ke ciki da kuma muradun bai daya za su samar da sakamako mai ɗorewa da kwanciyar hankali," in ji Erdogan.

Ya yi kira ga ƙasashen da ke da ƙarfin diflomasiyya, albarkatun tattalin arziki da kuma ikon yin magana da ɓangarori daban-daban su ɗauki "ƙarin rawar da za su taka" wajen haɓaka zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Erdogan ya kuma tabo batun rashin daidaiton tattalin arziki, yana mai cewa ba a cim ma burin da aka yi na tsammanin cewar hadewar duniya waje guda zai kawo walwala a ko’ina.

Ya ce bambancin samun kuɗi ya ƙaru, yayin da dogaro da fasaha da tattalin arziki ya zama sabbin fannoni na gasa.

"Domin a cim ma adalci a duniya a ƙarƙashin waɗannan yanayi masu canzawa, dole ne a raba nauyin da ya dace," in ji Erdogan, yana mai ƙara wa da cewa ya kamata a tabbatar da haƙƙin ƙasashe masu tasowa na ci gaba da samun kuɗin da suke buƙata.

Ya kuma yi tsokacin cewa dole ne tsarin duniya ya yi la'akari da sauyi a fannin tattalin arziki da siyasa a yankuna daban-daban.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da amfani da dangantakarta ta kasa da kasa da kuma gogewarta a fannin diflomasiyya ta bangarori daban-daban don tallafawa kokarin gyara tsarin kasa da kasa.

"Muna goyon bayan kokarin kawar da damar hawa kujerar na ki, a ba wa zababbun 'yan mambobi karfi mai yawa a tsarin yanke shawara da kuma karfafa rawar da Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ke takawa," in ji shi.

Ya ce hadin gwiwa tsakanin kasashe daga yankuna daban-daban tare da aiki da ka'idojin bai daya zai karfafa halacci da kuma ikon wakilci na tsarin kasa da kasa.

"Ba za a iya cim ma zaman lafiya na dindindin a duniyar yau ta hanyar ninka kungiyoyin da ba su da alaka da juna kuma ba sa sadarwa da juna ba," in ji Erdogan.

"Domin samun duniya mai adalci, dole ne mu hada kwarewa, iko da kuma bukatar dukkan yankuna daban-daban a kan manufa daya."

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da daukar nauyinta a kokarin gyara tsarin kasa da kasa, yana mai ambaton al'adar kasar, karfin diflomasiyya da kuma dangantakarta da yankuna daban-daban.