Shahararren malamin addinin Musulunci a Nijeriya kuma shugaban hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira da a gyara tsarin harkar siyasa a ƙasar, yana mai cewa yawaitar ƙage, sharri da ƙarya na ƙara lalata siyasa da kuma raba kan al’umma.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa siyasa ta koma fagen gaba, ƙiyayya da rushe mutuncin juna, maimakon ta zama hanyar hidima, haɗin kai da gasa ta gaskiya.
Ya ce a yau ana yawan ganin yaɗa jita-jita ba tare da tabbaci ba, ƙirƙirar labaran ƙarya domin ɓata suna, da kuma cin mutunci a kafafen sadarwa, lamarin da ke haifar da rarrabuwar kai tsakanin jama’a saboda son mulki.
Sheikh Daurawa ya kuma ce wannan hali yana jawo sakamako da suka haɗa da rashin amincewa tsakanin shugabanni da jama’a, ƙiyayya tsakanin ‘yan siyasa, da kuma lalacewar tarbiyyar matasa masu shiga siyasa. Ya ƙara da cewa hakan na kuma hana ci gaban ƙasa saboda yawan rikice-rikice.
Malamin ya jaddada cewa addini da hankali suna koyar da gaskiya, adalci da kiyaye mutuncin mutane, inda ya tunatar da cewa Musulunci ya hana ƙage, gulma da cin mutunci saboda suna rusa zaman lafiya da haɗin kai.
A cewarsa, siyasa mai kyau ita ce wadda ta ginu kan gaskiya, hujja ba zagi ba, kishin ƙasa ba son zuciya ba, da kuma haɗin kai maimakon rarrabuwar kai.
Sheikh Daurawa ya ce idan ‘yan siyasa suka gyara harsunansu da niyyarsu tare da guje wa sharri da ƙage, siyasa za ta koma hanyar ci gaba da zaman lafiya maimakon ta zama hanyar fitina da gaba.
Ya kammala da addu’ar Allah Ya shirya shugabanni da al’umma baki ɗaya.











