| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Sheikh Daurawa ya yi kira a gyara harkar siyasa a Nijeriya, ya yi gargaɗi kan ƙage da sharri
Ya ce a yau ana yawan ganin yaɗa jita-jita ba tare da tabbaci ba, ƙirƙirar labaran ƙarya domin ɓata suna, da kuma cin mutunci a kafafen sadarwa, lamarin da ke haifar da rarrabuwar kai tsakanin jama’a saboda son mulki.
Sheikh Daurawa ya yi kira a gyara harkar siyasa a Nijeriya, ya yi gargaɗi kan ƙage da sharri
Sheikh Daurawa ya wallafa wannan saƙo ne a shafinsa na Facebook. / Others

Shahararren malamin addinin Musulunci a Nijeriya kuma shugaban hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira da a gyara tsarin harkar siyasa a ƙasar, yana mai cewa yawaitar ƙage, sharri da ƙarya na ƙara lalata siyasa da kuma raba kan al’umma.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa siyasa ta koma fagen gaba, ƙiyayya da rushe mutuncin juna, maimakon ta zama hanyar hidima, haɗin kai da gasa ta gaskiya.

Ya ce a yau ana yawan ganin yaɗa jita-jita ba tare da tabbaci ba, ƙirƙirar labaran ƙarya domin ɓata suna, da kuma cin mutunci a kafafen sadarwa, lamarin da ke haifar da rarrabuwar kai tsakanin jama’a saboda son mulki.

Sheikh Daurawa ya kuma ce wannan hali yana jawo sakamako da suka haɗa da rashin amincewa tsakanin shugabanni da jama’a, ƙiyayya tsakanin ‘yan siyasa, da kuma lalacewar tarbiyyar matasa masu shiga siyasa. Ya ƙara da cewa hakan na kuma hana ci gaban ƙasa saboda yawan rikice-rikice.

Malamin ya jaddada cewa addini da hankali suna koyar da gaskiya, adalci da kiyaye mutuncin mutane, inda ya tunatar da cewa Musulunci ya hana ƙage, gulma da cin mutunci saboda suna rusa zaman lafiya da haɗin kai.

A cewarsa, siyasa mai kyau ita ce wadda ta ginu kan gaskiya, hujja ba zagi ba, kishin ƙasa ba son zuciya ba, da kuma haɗin kai maimakon rarrabuwar kai.

Sheikh Daurawa ya ce idan ‘yan siyasa suka gyara harsunansu da niyyarsu tare da guje wa sharri da ƙage, siyasa za ta koma hanyar ci gaba da zaman lafiya maimakon ta zama hanyar fitina da gaba.

Ya kammala da addu’ar Allah Ya shirya shugabanni da al’umma baki ɗaya.

Rumbun Labarai
Bayani dalla-dalla: Shin kotu ta soke rajistar jam'iyyar NDC ne a Nijeriya?
Bayan shekaru 22, Taron NATO ya dawo Ankara a wata duniya ta daban
Shugaba Tinubu ya ce Nijeriya na cikin jarabawa amma za ta warware lafiya
Pantami ya janye daga zaben fidda gwanin APC na gwamna a Gombe kan zargin take dokokin zabe
'Shugaban Kasa ya ce min za a bi tsarin ƙato-bayan-ƙato a fidda ɗan takarar gwamnan APC a Gombe'
Hukunce-hukuncen Kotu da makomar jam'iyyun adawa a Nijeriya
Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da shugabancin Jam'iyyar ADC na David Mark
Kotun Ƙolin Nijeriya ta rusa babban taron PDP wanda aka zabi Kabiru Turaki a matsayin shugaba
Danmajalisar Amurka na son a ƙwace shaidar ɗan ƙasa ta duk mai alaƙa da Tsaurin Ra'ayin Musulunci
Me ya sa Amurka ke komawa ga zamanin Yakin Duniya na II, da tunkarar masu motoci don kera makamai?
Ministan Kudin Benin Romuald Wadagni ya lashe zaben shugaban kasar
Wane ne Franck Biya da ake hasashen zai iya Shugaban Ƙasar Kamaru na gaba?
Wane tasiri shigar Yusuf Buhari siyasar Nijeriya za ta yi?
Rikicin cikin gida na Jam'iyyar ADC da makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya
Sabon Salo a Siyasar Nijeriya: Nazari kan Jihar Kano
Za a ci gaba da tsare El-Rufai yayin da kotu ta ɗage sauraron buƙatar neman beli zuwa 14 ga Afrilu
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara a Nijeriya ya fice daga PDP zuwa APC
Jam’iyyun Adawa a Nijeriya sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026, sun nemi a yi sabon gyara
Jajircewar Turkiyya a Afirka: Labarin haɗin-kai da kyakkyawan fata
Martanin duniya a yayin da Isra’ila ke rajistar mallake Gabar Yammacin Kogin Jordan